Matar wani gwamnan Arewa ta biya ma wata mara lafiya naira N1,300,000 kudin asibiti

Matar wani gwamnan Arewa ta biya ma wata mara lafiya naira N1,300,000 kudin asibiti

Uwargidar gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu, Zainab Bagudu ta biya kudi naira miliyan daya da dubu dari uku na wata yarinya mai shekaru goma sha shidda dake fama da cutar sikila, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito Hajiya Zainab ta gudanar da wannan abin alheri ne ta karkashin gidauniyar ta mai suna Medicaid Cancer Foundation, inda ta bayyana haka a ranar Litinin a garin Birnin Kebbi na jihar Zamfara.

KU KARANTA: Rikicin jihar Zamfara: Dakarun Soji sun bindige yan bindiga 20 sun kwato makamai

“Na biya dukkanin kudin da ake bukata don kulawa a Hadiza Bagudu da za ayi mata aikin sauyaa kugu akan kudi naira miliyan daya da dubu dari Uku.” kamar yadda ta Zainab ta shaida ma manema labaru.

Daga karshe Zainab ta yi fatan Allah ya bada nasara a aikin da za’ayi ma Hadiza, sa’annan tace zata cigaba da taimaka ma marasa lafiya, da ma sauran gajiyayyu mabukata.

Shi dai cutar sikila ana daukarsa ne mafi yawanci ta hanyar gado, ma’ana idan namiji yana dauke da ita, kuma mace ma na dauke da ita, akwai yiwuwar zasu haifui yaya masu wannan cuta, Allah ya karemu gaba daya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar NAIJ.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abin ya zafafa: Saraki sun ruga kotu, da rokon ta hana IGP, AGF da DSS tsige su, kuma ta kai musu

Abin ya zafafa: Saraki sun ruga kotu, da rokon ta hana IGP, AGF da DSS tsige su, kuma ta kai musu

Abin ya zafafa: Saraki sun ruga kotu, da rokon ta hana IGP, AGF da DSS tsige su, kuma ta kai musu
NAIJ.com
Mailfire view pixel