Rikicin jihar Zamfara: Dakarun Soji sun bindige yan bindiga 20 sun kwato makamai

Rikicin jihar Zamfara: Dakarun Soji sun bindige yan bindiga 20 sun kwato makamai

Dakarun runduna ta daya na mayakan Sojin Najeriya sun samu nasarar hallaka yan bindiga da ake zargin yaran Buharin Daji ne dai dai har guda ashirin, da suka yi kaurin suna wajen kashe kashe da sace sacen jama’a a tsakanin Zamfara da Kaduna.

Mataimakin Daraktan watsa labaru na rundunar, Kanal Muhammad Dole ne ya bayyana haka a karshen mako yayin wata ganawa da manema labaru, inda yace Sojojin sun kashe yan bindigan ne a karkashin aiki na musamman, Operation Idon raini.

KU KARANTA: Karyar karatu: Jami’an yaki da rashawa sun yi ram da shugaban kwalejin kimiyya da fasaha

“A yayin aikin Operation Idon raini, Dakarunmu sun kai samame zuwa mabuyar yan bindiga dake kauyen Jambirni a karamar hukumar Maru na jihar Zamfara, inda suka kashe guda ashiri, suka kama guda uku, sa’annan wasu suka tsere da rauni.” Ini shi.

Kaakaki Muhammadu ya cigaba da fadin: ‘Mun gano makamai da suka hada da bindigar AK47 guda hudu, wayar salula kirar Motorola, alburusai, bindigun toka da wasu wayoyin hannu guda uku da na’aurar caja wayoyi.”

Daga karshe yace rundunar na godiya ga jama’a dake basu muhimmai kuma sahihan bayanan sirri, haka zalika yace Sojoji sun zage damtse don kawo karshen ayyukan yan bindiga a jihar Zamfara, da ma sauran sassan kasar nan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel