Buhari ya gargadi Malaman Jami'a

Buhari ya gargadi Malaman Jami'a

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargadi dukkanin makarantun jami'a na kasar nan da su guji duk wani nau'i na cin hanci da rashawa, tada zaune tsaye da kuma lalata da dalibai wanda har kullum ke zubar da mutuncin harkar ilimi a Najeriya

Buhari ya gargadi Malaman Jami'a
Buhari ya gargadi Malaman Jami'a

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargadi dukkanin makarantun jami'a na kasar nan da su guji duk wani nau'i na cin hanci da rashawa, tada zaune tsaye da kuma lalata da dalibai wanda har kullum ke zubar da mutuncin harkar ilimi a Najeriya.

DUBA WANNAN: In kana duniya kasha kallo: An gano wani kashin kunkuru mai shekaru miliyan 150 a duniya

Shugaban kasan yayi wannan jawabin ne a wani taron yaye dalibai kashi na 29 da 30 na jami'ar Jos wanda akayi a filin wasa na Jeremiah T. Useni dake cikin jami'ar a karshen makon da ya gabata.

Shugaban kasar yace gwamnati zata hukunta duk wata jami'a da tayi kasa a guiwa gurin magance matsalar lalata da dalibai da malamai ke yi.

A jawabin da mai wakiltarshi yayi, zababben sakataren kungiyar jami'o'i ta kasa, farfesa Rasheed Abubakar, shugaban kasar yace dole ne kowacce jami'a ta kwatanta gaskiya, nagarta da rikon amana kuma tare da kare dokoki domin taka rawar gani gurin habaka tattalin arziki, siyasa da al'adun Najeriya.

Jimillar dalibai 18,348 aka yaye a jami'ar wanda ya hada da masu shaidar difloma, digiri na farko, digiri na biyu da kuma digirin digirgir.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel