‘Yan APC 3 daga jihar Kano sun yi hatsarin mota a hanyar su ta zuwa taron jam’iyyar a Abuja

‘Yan APC 3 daga jihar Kano sun yi hatsarin mota a hanyar su ta zuwa taron jam’iyyar a Abuja

- Allah ya yiwa wasu ‘yan jam’iyyar APC uku (3) rasuwa, ciki har da wani kansila daga karamar hukumar Gwale

- Sun gamu da ajalin su bayan motar su tayi hatsari a garin Zaria a hanyar su ta zuwa Abuja domin halartar taron jam’iyyar APC

- Sun yi hatsarin ne a jiya, Asabar, 23 ga watan Yuni, 2018

A jiya, Asabar, ne wasu ‘yan jam’iyyar APC daga jihar Kano suka gamu da ajalin su bayan motar su kirar Honda CRV tayi hatsari a garin Zaria a hanyar su ta zuwa wurin taron zaben shugabannin jam’iyyar APC.

Jaridar Premium Times ta rawaito cewar, daga cikin mutanen uku akwai kansilan mazabar Diso dake karamar hukumar gwale da kuma abokan sa biyu, Abdullahi Idris da Abubakar Diso.

‘Yan APC 3 daga jihar Kano sun yi hatsarin mota a hanyar su ta zuwa taron jam’iyyar a Abuja
Shugaba Buhari a wurin taron jam'yyar APC

Jaridar ta bayyana cewar mutanen uku sun bar Kano da sanyin safiyar ranar Asabar domin samun halartar taron zaben sabbin shugabannin jam’iyyar ta APC.

Wani shaidar gani da ido, Murtala Lawan, ya shaidawa Premium Times cewar, motar dake dauke da mutanen ta fadi a daidai kauyen Amaryawa dake daf da garin Zaria.

DUBA WANNAN: Hotuna da bidyo: Hukumar ‘yan sanda ta ankarar da jama’a wasu sabbin dabaru da ‘yan fashi suka bullo da su

Iyalin Kansilan, tab akin wani dan uwan sa, sun tabbatar da afkuwar hatsarin tare da bayyana cewar marigayin bai dade da dawowa daga kasar Saudiyya ba inda ya je aikin Umrah.

Babban limamin masallacin gidan sarkin Kano, Farfesa Sani zaharaddeen, ya sallaci mamatan da misalign karfe 4:30 na yammacin jiya, Asabar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel