Shin wanene sabon Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole

Shin wanene sabon Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole

- Oshiomhole ya dade yana gwagwarmayar kwadago kafin shiga siyasa

- Kwamared Oshiomhole ya fito takarar Gwamna ne a 2007 karkashin AC

- Kotu ta ba Oshiomhole nasara inda ya kammala wa’adin sa a cikin 2016

Jiya kun ji labari cewa Kwamared Adams Oshiomhole ne ya zama sabon shugaban Jam’iyyar APC mai mulki. Dalilin haka ne mu ka kawo maku wasu abubuwan da ya kamata ku sani game da sabon shugaban na APC.

Shin wanene sabon Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole
Sabon Shugaban APC Adams Oshiomhole tare da Buhari

Asalin tsohon Gwamnan Musulmi ne kuma an haife sa ne a kusa da Garin Auchi da ke Jihar Edo shekaru 66 da su ka wuce.

Ga kadan daga labarin sabon shugaban na APC na kasa:

1. Gwagwarmaya a kungiyar kwadago

Tun a 1970s Kwamared Adams Oshiomhole yake fafatuka a matsayin Jagoran Ma’aikata inda a 1999 ya zama Shugaban Kungiyar kwadago na Kasar nan. Oshiomhole ne ya shiga ya fita aka kara albashin Ma’aikata a lokacin Obasanjo kafin abubuwa su yi tsami.

2. Zama Gwamnan Jihar Edo

A 2007 ne Adams Oshiomhole yayi takarar Gwamnan Jihar Edo inda ya sha kasa wajen ‘Dan takarar Jam’iyyar PDP Oserheimen Osunbor. Sai dai daga baya kotu ta soke zaben ta kuma ba Oshiomhole na Jam’iyyar AC nasara a karshen shekarar 2008.

3. Rayuwar aure da rashin matar sa

Asalin Adams Oshiomhole Musulmi ne sai dai daga baya Matar sa mai suna Clara ta sa shi ya zama Kirista. Daga baya dai Clara ta rasu bayan tayi fama da rashin lafiya. Bayan wani lokaci ne ya auri wata tsaleleiyar Budurwa mai suna Lara Fortes ‘Yar kasar waje.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel