Taron siyasa a Najeriya, Habasha da Zimbabwe: An kaiwa shuwagabannin Afirka biyu hari, na uku ya wanye lafiya

Taron siyasa a Najeriya, Habasha da Zimbabwe: An kaiwa shuwagabannin Afirka biyu hari, na uku ya wanye lafiya

- Anyi taron siyasa a kasashen Afirka guda uku, biyu bam ya fashe, kuma an mutu

- Shugaban kasar Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa ya tsallake rijiya da baya sakamakon harin Bam da ya tsere a rali a birnin Bulawayo

- Mista Mnangagwa yace wani abu mai fashewa ya tashi a tazara kadan daga inda nake, amma lokacina bai yi ba

Taron siyasa a Najeriya, Habasha da Zimbabwe: An kaiwa shuwagabannin Afirka biyu hari, na uku ya wanye lafiya
Taron siyasa a Najeriya, Habasha da Zimbabwe: An kaiwa shuwagabannin Afirka biyu hari, na uku ya wanye lafiya

Shugaban kasar Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa ya tsallake rijiya da baya sakamakon harin Bam da ya tsere a rali a birnin Bulawayo.

Mista Mnangagwa yace wani abu mai fashewa ya tashi a tazara kadan daga inda nake, amma lokacina bai yi ba.

Wani video daga sitadiyum din White City ya nuna fashewar wani abu kusa da Mista Mnangagwa a lokacin da yake sauka da mumbari bayan ya gama jawabi ga magoya bayan shi.

Shugaban dai bai samu wani rauni ba. State TV ta bada rahoton cewa mataimakin shugaban kasa Kembo Mohadi ya samu rauni a kafa.

Mista Mnangagwa yace ya ziyarci wadanda suka samu rauni a asibiti. Ya kushe harin a matsayin rashin hankali, a inda daga baya ya roki hadin kai.

DUBA WANNAN: Ja'in-ja kan wasu kujerun a taron APC

Shugaban kasar dai yaje Bulawayo, babban birni na biyu a Zimbabwe kuma yan adawa, domin kamfen din jam'iyyar Zanu-PF a zaben da ke gabatowa na 30 ga watan yuli.

"Mutane sun fara gudu a rude sannan motocin shugaban kasar suka bar gurin a guje" Wani mai rahoton AFP ya ruwaito.

Mai magana da yawun shugaban kasan, George Charamba ya sanar da jaridar Herald ta Zimbabwe cewa mutane 8 ko 9 ne suka samu rauni, da yawan su an kaisu asibiti kuma an sallamesu.

"Mataimakin shugaban kasa Mohadi yana jinyar raunin kafar shi, amma yana samun sauki." a yanda yace.

Matar mataimakin shugaban kasar, Marry Chiwenga, itama ance ta samu raunika kuma anga hotunan da shugaban kasan ya ziyarce ta a asibiti.

A Ethiopia ma, watau Habasha dai, ana cikin irin wannan taro bam ya fashe, ya kashe mutum daya amma shugaban ya sha shima.

Ana irin wannan bikin siyasar yanzu haka a Abuja, fatanmu a wanye lafiya

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel