Kofin duniya: 'Yan Najeriya za su sha ruwan kudi bayan lallasa kasar Iceland

Kofin duniya: 'Yan Najeriya za su sha ruwan kudi bayan lallasa kasar Iceland

- Yan kwallon Najeriya za'a ba su kyautar kudi sakamakon cin Iceland da suka yi

- Za'a ba kowane dan wasan kasa $ dubu 20 ne kyauta

- Yanzu haka dai Najeriya ta fara sinsinar tsallake rukunin ta na E

Mun samu cewa sakamakon doke kasar Iceland da yan wasan Najeriya suka yi jiya yanzu kowane dan kwallon kasar zai samu kyautar Dalar Amurka dubu 20 daga kamfanin Scandinavian.

Kofin duniya: 'Yan Najeriya za su sha ruwan kudi bayan lallasa kasar Iceland

Kofin duniya: 'Yan Najeriya za su sha ruwan kudi bayan lallasa kasar Iceland

KU KARANTA: PDP a Bayelsa ta tozarta Atiku

Wannan dai kamar cikon alkawari ne daga kamfanin da ya daukar wa kansa cewa duk wasan da 'yan kasar suka ci zai ba su kyautar kudi.

NAIJ.com ta samu cewa a jiya ne dai 'yan wasan suka kayatar da 'yan kasar sosai bayan doke kasar Iceland da ci 2 da nema.

Fitaccen dan wasan gaban nan Ahmad Musa ne dai ya samu nasarar lallasa kasar da wasu kayatattun ciya-ciyai bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Wani miji ya silale cikin asibiti kawai domin tarawa da matarshi mai jinya

Wani miji ya silale cikin asibiti kawai domin tarawa da matarshi mai jinya

Wani miji ya silale cikin asibiti kawai domin tarawa da matarshi mai jinya
NAIJ.com
Mailfire view pixel