Ba mu da tanadin Fulotai domin kafa Yankunan Kiwon Shanu - Jihar Ebonyi ga Gwamnatin Tarayya

Ba mu da tanadin Fulotai domin kafa Yankunan Kiwon Shanu - Jihar Ebonyi ga Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin jihar Ebonyi karkashin jagorancin Dave Umahi, ta shaidawa gwamnatin tarayya cewa ba ta da tanadi na Fulotai domin kafa yankunan kiwon shanu.

Kwanaki kadan da suka gabata ne gwamnatin tarayya ta bayar da sanarwa kafa yankuna 10 na kiwon shanu cikin wasu sassa na jihohin kasar nan da ta jeranto har da jihar Ebonyi.

Sai dai a yayin ganawa da manema labarai bayan zaman majalisar zantarwa na jihar Ebonyi, Kwamishinan noma Barrista Ikechukwu Nwobo ya shaidawa gwamnatin tarayya cewa, ba bu tanadi na Fulotai domin kafa yankunan kiwon shanu a jihar.

Ba mu da tanadin Fulotai domin kafa Yankunan Kiwon Shanu - Jihar Ebonyi ga Gwamnatin Tarayya

Ba mu da tanadin Fulotai domin kafa Yankunan Kiwon Shanu - Jihar Ebonyi ga Gwamnatin Tarayya

Nwobo yake cewa, majalisar zantarwa ta jihar ta bayyana fushin ta dangane da rahotanni dake yaduwa a kafofin watsa labarai da cewar jihar Ebonyi ta tanadi yankuna domin kafa garkunan kiwon Shanu.

KARANTA KUMA: Jam'iyyar PDP ta gargadi Gwamnatin Tarayya kan Yankunan Kiwon Shanu

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, Kwamishina ya jaddada cewa jihar Ebonyi ba ta yi tanadin Fulotai domin kafa yankunan kiwon Shanu ba inda ya ce garkunan kiwo na jihohin Arewa ne ma su mallakin Shanu.

Majalisar zantarwa ta jihar ta yanke shawara ta tabbatar da cewa ba bu wani yankin kiwon shanu a jihar kuma ba ta da shiri na samar da yankunan a duk fadin jihar kamar yadda kwamishinan ya bayyana.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
2019: Ba za mu goya ma Buhari baya ba – Gamayyar tsoffin ýan bindiga

2019: Ba za mu goya ma Buhari baya ba – Gamayyar tsoffin ýan bindiga

2019: Ba za mu goya ma Buhari baya ba – Gamayyar tsoffin ýan bindiga
NAIJ.com
Mailfire view pixel