Babban rashi: Sarkin fadar masarautar Kano ya rasu yana da shekaru 107

Babban rashi: Sarkin fadar masarautar Kano ya rasu yana da shekaru 107

Sarkin Fadar masarautar Kano, Alhaji Sule Gaya ya rasu a ranar Alhamis, 21 ga watan Yuni bayan wata gajeruwar rashin lafiya da yayi fama da shi, kamar yadda kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito mai magana da yawun iyalan Sarkin Fada, Hajiya Amina Abdullah ce ta sanar da mutuwar tasa, inda tace za’ayi jana’izarsa a ranar Juma’a, 22 ga watan Yuni da misalin karfe 10 na safe a fadar mai martaba Sarkin Kano.

KU KARANTA: Kashe kashe a Zamfara: Gwamnatin Buhari ta caccaki gwamna Abdul Aziz Yari

Babban rashi: Sarkin fadar masarautar Kano ya rasu yana da shekaru 107
Sarkin Fada

An haifi Sarkin Fada a garin Gaya, cikin karamar hukumar Gaya ta jihar a Kano a shekarar 1925, ya rasu yana da shekaru dari da bakwai, 107, ya bar yaya, jikoki da tattaba kunne, daga cikinsu akwai Dakta Binta Sulaiman, Malama a tsangayar koyar da aikin jarida na jami’ar Bayero, Baffa Sule Gaya tsohon shugaban kwalejin kimiyya da fasaha na Kano.

Sule Gaya na daga cikin tsofaffin yan boko kuma yan siyasar jihar arewa, ya halarci makarantar Firamari a tsakanin 1932-1938 ya shiga makarantar middle ta Kano a tsakanin 1938-1943, sai Katsina Teacher Training College 1947-1952.

Babban rashi: Sarkin fadar masarautar Kano ya rasu yana da shekaru 107
Sarkin Fada

Dagabisani ya zama karamin headmaster a makarantar primary Birnin Kudu 1952-1953, A shekarar 1956 aka zabe shi Dan Majalisar jihar arewa ya kuma taba rike mukamin parliamentary Secretary a 1957, inji Dandalin tarihin magabata.

A zamaninsa, Sarkin Fada ya taba zama dan majalisa dake wakiltar yankin Arewa a zamanin mulkin Turawa, haka zalika ya taba zama ministan sufiyo a zaman mulkin mulkin Sir Ahmadu Bello Sardauna Firimiyan Arewa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel