Ruwan da ya dake ka: Dan Abiola ya shiga APC, ya tsaya takarar wata kujera a jam’iyyar

Ruwan da ya dake ka: Dan Abiola ya shiga APC, ya tsaya takarar wata kujera a jam’iyyar

Abdulmumin Abiola, dan gidan marigayi Abiola ya shiga cikin sahun masu neman takarar kujerar shugaban matasan jam’iyyar APC a zaben da zata yin a shugabanni a karshen mako.

Abdulmumin ya ce ya shiga takarar neman kujerar ne saboda imanin da ya yi da manufar jam’iyyar APC na son kawo cigaba ga Najeriyua da mutanen ta.

Ko a kwanakin baya saida naij.com ta kawo maku labarin yadda Babban dan marigayi Abiola, Kola Abiola, ya ce ba zai taba manta yadda tsohon shugaban kasa Jonathan ya yi kememe a kan batun karrama mahaifin sa ba duk da sau uku (3) yana rokon shi a kan hakan.

Ruwan da ya dake ka: Dan Abiola ya shiga APC, ya tsaya takarar wata kujera a jam’iyyar

Abdulmumin Abiola

A kwanakin baya ne gwamnatin Buhari ta karrama marigayi Abiola da lambar girma ta GCFR da kuma mayar da ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar dimokraddiya ta Najeriya.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa nake farinciki da binciken da EFCC ke yi min – Babachir David Lawal

Abiola ne ya lashe zaben shekarar 1993 amma gwamnatin soji ta Ibrahin Badamasi Babangida (IBB) ta hana shi hawa mulkin.

Da yake Magana a wani shirin gidan talabijin din Channels a jiya, Alhamis, Kola, ya ce ya nemi tsohon shugaban kasa Jonathan ya karrama mahaifin sa da lamabar girma ta GCFR amma saboda wasu dalilai na siyasa ya ki yin hakan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
2019: Atiku ya yi tutiya da kwarewarsa a wata matsala da take addabar Najeriya

2019: Atiku ya yi tutiya da kwarewarsa a wata matsala da take addabar Najeriya

2019: Atiku ya yi alfahari da kwarewar sa a warware wata matasalar da ya ce tafi damun Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel