Gwamanatin tarayya zata gina wuraren kiwo 94 a jahohi 10

Gwamanatin tarayya zata gina wuraren kiwo 94 a jahohi 10

- Wuraren kiwo 94 gwamnati zata samar don magance rikicin makiyaya

- Rikici tsakanin manoma da makiyaya ya kasance hanyar asarar rayuka da dukiyoyin mutane da yawan gaske

- Ana kyautata zaton bullo da wannan shiri zai taimaka wajen magance fadace-fadace tsakaninsu

Majalisar zartarwar tattalin kasa karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ta amince da wani tsari da aka bullo da shi don habaka kiwo, shirin da zai dauki tsawon shekaru 10 da ake sa rai zai lakume N179b.

Gwamanatin tarayya zata bullo da wani shiri da gina wararen kiwo don magance fadan manoma da makiyaya
Gwamanatin tarayya zata bullo da wani shiri da gina wararen kiwo don magance fadan manoma da makiyaya
Asali: Depositphotos

Ana dai sa rai gwamnatin tarayya zata bayar da kimanin N70b nan da watanni 11 kafin karshen mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Duka dai gwamnonin jahohin kasar nan mambobi ne a majalisar, kuma za’a samar da wuraren kiwon ne guda 94 a jahohi 10 da suka kunshi; Adamawa, Benue, Edo, Ebonyi, Kaduna, Nasarawa, Oyo, Plateau, Taraba, da kuma Zamfara.

Amma ya zuwa yanzu jahohin Benue da Nasarawa ne ke kan gaba da za’a fara samar da wuraren kiwon nan da kowanne lokacin.

KU KARANTA: Yadda wata yarinya ‘yan shekara 12 da ta ceci rayukan mutane 300 a Zimbabwe

Wannan na fitowa ne daga bakin wakilan majalisar yayin zantawa da maneman labarai a Abuja, wakilan sun hada da gwamnan jihar Benue Samuel Ortom da ministan noma da cigaban karkara Audu Ogbeh da shugaban shirin gina wuraren kiwon Dr. Andrew Kwasari.

Audu Ogbeh ya bayyana cewa “Kiwo a fili ba abu ne da zai dore ba” Idan aka samu nasarar gina wuraren kiwon, makiyaya ne zasu amfana sosai nan da shekaru masu zuwa.

Sannan ya ce gwamnatin tarayya bata da niyyar kwacewa kowa muhallinsa domin mayar da shi wurin kiwo.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel