Ka janye sojoji daga Maiduguri, ka tura ‘yan sandan SARS –Kungiyar kishin Najeriya ga Buhari

Ka janye sojoji daga Maiduguri, ka tura ‘yan sandan SARS –Kungiyar kishin Najeriya ga Buhari

Wata kungiya mai rajin kishin Najeriya da aka fi sani da “Every Nigerian Do Something Positive Development Initiative” ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci sojoji das u koma bariki tare da bawa ‘yan sanda dammar yaki da aiyukan ta’addanci na kungiyar Boko Haram.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar, kungiyar tayi wannan kiran ne yayin wata zanga-zangar lumana da ta gudanar a majalisar kasa yau, Talata, a Abuja.

Ka janye sojoji daga Maiduguri, ka tura ‘yan sandan SARS –Kungiyar kishin Najeriya ga Buhari

Wasu masu zanga-zanga

Kungiyar ta ambaci ‘yan sandan SARS masu aikin yaki da fashi da makami da kuma masu rakiyar manyan attajirai da ‘yan siyasa a matsayin ‘yan sandan day a kamata Buhari ya tura Maiduguri domin kare rayuka da dukiyar jama’a.

Jagoran masu zanga-zangar, Dakta Perry Brimah, ya yi kira da a mayar da sojoji bariki tare da bayyana cewar kundin tsarin mulkin Najeriya bai ambaci sojoji a matsayin jami’an tsaron da zasu yi yaki da ta’addanci a cikin kasa ba.

DUBA WANNAN: Da dumin sa: Dakarun soji sun yi nasarar gungun wasu ‘yan ta’adda a jihar Benuwe

Babu kowa daga cikin shugabannin majalisar da zai yiwa masu zanga-zangar jawabi kasancewar ‘yan majalisar sun tafi hutu na tsawon sati 6.

Wani daga cikin jami’an ‘yan sanda da suke kula da masu zanga-zangar y ace kungiyar na gudanar da zanga-zangar lumana ne a saboda haka babu ruwan su da bukatar da suke nema wurin gwamnati.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Tsare ‘Dan Jarida: Atiku Abubakar yayi kira ga ‘Yan Sandan Najeriya da babbar murya

Tsare ‘Dan Jarida: Atiku Abubakar yayi kira ga ‘Yan Sandan Najeriya da babbar murya

Tsare ‘Dan Jarida: Atiku Abubakar yayi kira ga ‘Yan Sandan Najeriya da babbar murya
NAIJ.com
Mailfire view pixel