Masha Allah: Buhari ya bullo da hanyoyi 6 na kawo karshen kashe kashe tsakanin Manoma da Makiyaya

Masha Allah: Buhari ya bullo da hanyoyi 6 na kawo karshen kashe kashe tsakanin Manoma da Makiyaya

Gwamnatin Najeriya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bullo da wasu sabbin hanyoyi da zata bi don ganin ta kashe wutar rikici da yaki ci yaki cinyewa a tsakanin Fulani makiyaya da manoma a birane da kauyukan kasar nan.

Jaridar Premium Times ta ruwaito an bayyana wadannan dabaru ne a ranar Talata, 19 ga watan Yuni a babban birnin tarayya Abuja, ta hannun wani babban jami’I a kwamitin tattalin arzikin kasa, NEC, Andrew Kwasari.

KU KARANTA: Yansandan Najeriya sun yi ma wasu gagararrun yan bindiga shigo shigo ba zurfi

A jawabinsa, Andrew yace hanyoyin magance kashe kashe da asarar dukiyoyi a tsakanin makiyaya da manoma sun kunshi; inganta tattalin arziki, samar da sulhu, bin doka da ka’ida, tallafi da agaji, samar da ingantattun bayanai da kuma watsa labaru.

Masha Allah: Buhari ya bullo da hanyoyi 6 na kawo karshen kashe kashe tsakanin Manoma da Makiyaya
Shanu

A karkashin wannan sabon salo da gwamnatin Buhari ta kirkiro, za’a gina gandun kiwon dabbobi a jihohi guda goma da za’a fara gwaji dasu, jihohin kuwa sune, Kaduna, Benuwe, Adamawa, Ebonyi, Oyo, Filato, Taraba, Zamfara, Edo da Nasarrawa.

Kowanne gandun kiwo da za’a gina zai kunshi akalla shanu Talatin zuwa dari uku, inda ake sa ran killace akalla shanu dubu daya a kowanne jihar da za’ayi amfani da ita wajen gwada wadannan kyawawan tsare tsare da ake sa ran zasu lakume kudi naira biliyan 70 cikin shekaru uku.

Sai dai Kwasari yace ana sa ran idan tsare tsaren nan suka tafi yadda ya kamata, yawan adadin madaran nono da ake samu daga shanu zai karu zuwa lita miliyan dari biyu a shekarar farko, inda zai haura miliyan dari bakwai a shekaru hudu masu zuwa.

Dayake nasa jawabi, Ministan gona, Audu Ogbeh ya bayyana cewa gwamnati ta himmatu wajen kawo karshen rikicin manoma da makiyaya, kuma wannan tsari zai fara aiki nan bada jimawa ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel