Buhari ya sharewa matasa fagen hawa kujerar mulki

Buhari ya sharewa matasa fagen hawa kujerar mulki

Shugaban kungiyar masu rajin kare manufofin Buhari, Injiniya Muftahu Aliyu Hassan yace bayan kaddamar da dokar ba matasa damar shiga harkar siyasa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rigada ya sharewa matasa fagen da zasu kama mukaman siyasa.

Hassan dan takarar kujerar majalisar wakilai karkashin leman APC, inda zai wakilci mazabar Tarauni na jihar Kano, yace wanan cigaban ya nuna cewa lokaci yayi da za’a dama da matasa ta hanyar amfani da damar da aka basu domin su kawo chanji mai kyau.

“Sabuwar dokar kalubale ne aka jefawa matasan Najeriya, lokaci yayi da zamu tabbatar da muhimmancin matasan Najeriya,” inji shi.

Buhari ya sharewa matasa fagen hawa kujerar mulki
Buhari ya sharewa matasa fagen hawa kujerar mulki

“Koda dai bamu da masaniya kan sauran abubuwa da ka iya kawo cikas ga yunkurin, yin amfani da damar da aka bamu ta hanyar fitowa takara shine hanya guda da zamu godew shugaban kasa Muhammadu Buhari,” cewar shi.

A halin da ake ciki, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ba zai gana da mambobin sabuwar jam'iyyyar PDP ba (nPDP) duk da barazanar da su keyi na cewa za su fice daga jam'iyyar ta APC.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin kasar Swiss ta dawo wa Najeriya da dala miliyan $370

Sunyi zargin cewa an mayar da su saniyar ware a jam'iyyar ta APC kuma muddin ba'a basu damar da ganawa da shugaba Muhammadu Buhari ba, za su dauki matakin sauya sheka zuwa wata jam'iyyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel