'Yan kwallon kafan Saudiyya sun sauka lafiya bayan jirgin su ya kama da wuta a sararin samaniya

'Yan kwallon kafan Saudiyya sun sauka lafiya bayan jirgin su ya kama da wuta a sararin samaniya

- Jirgin saman da ke dauke da kungiyar kwallon kafa ta Saudiyya ya kama da wuta a sararin samaniya

- Duk da hakan, jirgin ya sauka lafiya a filin tashin jiragen sama na Rostov-on-Don kuma dukkan yan wasan suna lafiya

- Kamfanin jiragen sama na Rossiya ya ce tsuntsu ce ta shige cikin daya daga cikin injinan jirgin kuma ta haifar da matsalar

Jirgin saman da ke dauke da kungiyar kwallon kafa na kasar Saudiyya ya sauka lafiya a garin Rostov-on-Don inda za su kara da kasar Uruguay a yau Laraba 19 ga watan Yuni bayan rahotannin da aka samu cewa fuka-fukin jirgin ya kama da wuta yayin da suke sararin samaniya.

Kungiyar kwallon kafa ta Saudiyya sun isa Rasha lafiya bayan jirgin su ya kama da wuta a sararin samaniya
Kungiyar kwallon kafa ta Saudiyya sun isa Rasha lafiya bayan jirgin su ya kama da wuta a sararin samaniya

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya ce ba zai gana da mambobin nPDP ba, ya bayar da dalilinsa

Hukumar kula da kwallon kafa na Saudiyya ta bayar da sanarwa da shafin ta na twitter inda ta ce "muna son mu tabbatar wa kowa cewa mambobin kungiyar kwallon kafa na Saudiyya suna nan lafiya duk da tangardar daya daga cikin injinan jirgin saman su ya samu, sun sauka a filin tashin jirage na Rostov-on-Don inda za su karasa zuwa masaukin su."

Kungiyar kwallon kafa ta Saudiyya sun isa Rasha lafiya bayan jirgin su ya kama da wuta a sararin samaniya
Kungiyar kwallon kafa ta Saudiyya sun isa Rasha lafiya bayan jirgin su ya kama da wuta a sararin samaniya

Kungiyar kwallon kafan ta nuna hotunan yan wasan suna murmushi yayin da suka fitowa daga jirgin saman da daren Litinin sai dai ba'a bayar da cikaken bayanin irin matsalar da injin jirgin ya fuskanta ba duk da cewa akwai bidiyo da aka dauka daga cikin jirgin inda ya hayaki na fitowa daga daya daga cikin fuka-fukin jirgin.

Sanarwa na farko ta kamfanin jirgin saman na Rossiya ta fitar ya ce tsuntsu ne ya shiga cikin injin jirgin ya kuma haifar da matsalar sai dai sunce dukkan injinan biyu na aiki lokacin da jirgin ya sauka a Rostov-on-Don.

A wasan su ta farko Saudiyya ta sha kaye wajen Rasha inda ta doke ta da ci 5 - 0 da aka buga makon da ya gabata a garin Moscow, yanzu kuma zasu kara da kasar Uruguay.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel