Gyaran Najeriya sai an wahala daman - Inji Shugaba Buhari

Gyaran Najeriya sai an wahala daman - Inji Shugaba Buhari

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci karin hakuri daga 'yan Najeriya domin a cewar sa an jefa kasar cikin mawuyacin hali kafin zuwan sa kuma daman indai za'a yi gyara to dole ne sai an wahala.

Shugaban ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar barka da Sallah da ya aikewa 'yan Najeriya dauke da sa hannun mai taimaka masa na musamman ta fannin harkokin yada labarai, Garba Shehu.

Gyaran Najeriya sai an wahala daman - Inji Shugaba Buhari
Gyaran Najeriya sai an wahala daman - Inji Shugaba Buhari

KU KARANTA: Buhari na yiwa daukacin 'yan Najeriya barka da Sallah

Legit.ng ta samu cewa sai dai a cikin sanarwar, shugaban ya kara da cewa amma abun farin ciki shine wahalar da 'yan kasar ke sa ta dan wani lokaci ne kuma komai zai wuce nan ba da dadewa ba.

A wani labarin kuma, Wasu dattijan Najeriya a makon da ya gabata sun bukacin shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari da ya gaggauta tsige shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watau Independent National Electoral Commission (INEC) mai suna Farfesa Mahmoud Yakubu.

Wadanda suka yi kiran dai su ne Air Commodore Nkanga Idongesit da Chief Edwin Clark daga kudu maso kudancin Najeriya, Chief Ayo Adebanjo daga kudu maso yammacin Najeriya, Chief Chukwuemeka Ezeife daga kudu maso gabashin Najeriya, da kuma Air Commodore Dan Suleiman daga Arewa ta tsakiyar Najeriya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel