Hukumar INEC ta haramta amfani da wayar hannu a wurin zabe, ta bayyana dalili

Hukumar INEC ta haramta amfani da wayar hannu a wurin zabe, ta bayyana dalili

Hukumar zabe mai zaman kan ta (INEC) tayi gargadin cewar ba zata amince da amfani da wayar hannu a wurin kada kuri’a a zaben gwamna da za a yi a jihar Osun ranar 22 ga watan Satumba ba.

Kwamishinan INEC, Mista Olusegun Agbaje, ne ya yi wannan gargadi a garin Osogbo, babban birnin jihar, yayin wata ganawa da wakilan jam’iyyu dake da ‘yan takara a zaben mai zuwa.

Agbaje ya bayyana cewar INEC ta dauki wannan mataki ne bayan gano makarkashiyar da wasu ‘yan siyasa ke yi domin aikata magudin zabe. Ya kara da cewa, hukumar INEC dole ta dauki matakan dakile duk wani yunkuri da kan iya kawo nakasu ga tsaftar zaben da take shiryawa.

Hukumar INEC ta haramta amfani da wayar hannu a wurin zabe, ta bayyana dalili
Hukumar INEC ta haramta amfani da wayar hannu a wurin zabe, ta bayyana dalili

Ya kara da bayanin cewar, wasu ‘yan siyasa dake da niyyar bayar da kudi domin a zabi jam’iyyar su, sun bukaci masu kada kuri’a das u dauki hoton kuri’ar su bayan dangwalawa domin tabbatar da sun zabi abinda aka basu kudi su zaba.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun shammaci wasu masu garkuwa da mutane, sun kashe 3 daga cikin su

Kwamishinan yace wannan tsarin ya sabawa dokokin zabe tare da bayyana cewar hukumar INEC zata gurfanar da duk mai kada kuri’a da aka samu yana daukan hoton kuri’ar sa kafin ko bayan dangwalawa.

Agbaje ya lisafo ragowar dokokin zabe ga wakilan jam’iyyun tare da shaida masu cewar hukumar INEC ba zata ragawa duk mutum ko jam’iyyar da aka samu da laifin sabawa dokokin ba.tau

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel