Baku da hurumin binciken manyan laifuka – Kotu ta yiwa majalisa tuni a kan iyakar ikon ta

Baku da hurumin binciken manyan laifuka – Kotu ta yiwa majalisa tuni a kan iyakar ikon ta

Wata babbar kotun gwamnatin tarayya dake Abuja ta shaidawa majalisar wakilai cewar, bat a da hurumin binciken manyan laifuka ko kuma wanke wani daga zargin aikata laifi.

A wani hukunci da alkalin kotun, Gabriel Kolawole, ya yanke ranar Talata, ya ce azarbabin majalisa na shiga harkar binciken mutanen da ake zargi da aikata manya laifuka, ba daidai bane tare da bayyana cewar akwai hukumomin dake da alhakin binciken manyan laifuka.

Baku da hurumin binciken manyan laifuka – Kotu ta yiwa majalisa tuni a kan iyakar ikon ta
Majalisar Wakilai

Alkalin ya yanke wannan hukunci ne bayan wata kara mai lamba FHC/ABJ/CS/163/2009 da lauya, Festus Keyamo, ya shigar gaban kotun yana mai neman kotun ta tilasta shugabancin majalisar samar da bayani a kan badakalar sayen wasu motoci samfurin Peugeot guda 380 a shekarar 2008.

DUBA WANNAN: Alade mai nasibi ya hangowa Najeriya nasara a gasar cin kofin Duniya (Hotuna)

Saidai bayan shugaban majalisar wakilai a wancan lokacin, Oladimeji Bankole, ya mika korafin Keyamo ga kwamitin majalisar, sai suka bukaci a binciki Keyamo inda ya samo takardun shaidun dake hade da wasikar da ya aikowa majalisar tare da yin kira ga babban sifeton ‘yan sanda day a binciki lauyan.

A hukuncin da mai shari’a Kolawole ya yanke, ya dakatar da hukumar ‘yan sanda da ta DSS daga yin biyayya ga umarnin majalisa na bincikar Keyamo.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel