Makiyaya sun salwantar da Rayukan Mutane 5 a jihar Nasarawa

Makiyaya sun salwantar da Rayukan Mutane 5 a jihar Nasarawa

A ranar Talatar da ta gabata ne wani Manomi dan Kabilar Tibi tare da 'ya'yayensa uku suka sheka lahira a sakamakon wani hari na Makiyaya da suka kai kauyen Antsa dake karamar hukumar Keana a jihar Nasarawa.

Wannan hari ya afku ne jim kadan bayan da makiyaya suka kai hari kan wasu manoma yayin da suke tsaka da aiki a gonakin su dake kauyen Gada Biu a karamar hukumar Obi ta jihar inda suka salwantar da rayuwar wani mutum guda daya.

Makiyaya sun salwantar da Rayukan Mutane 5 a jihar Nasarawa

Makiyaya sun salwantar da Rayukan Mutane 5 a jihar Nasarawa

Rahotanni kamar yadda shafin jaridar The Nation ya bayyana, wannan hari ya gadar wa da mutane kimanin 20 raunuka masu girman gaske da a halin yanzu suke kwan-kwance a gadajen Asibiti.

KARANTA KUMA: Za a sake Karrama Wasu 'Yan Najeriya - Boss Mustapha

A yayin ganawa da menama labarai wani mashaidin wannan hari da ya afku a kauyen Antsa, Dennis Utsa ya bayyana cewa wannan ibtila'i mai munin gaske ya afku ne da misalin karfe 10.00 na safiyar ranar Talatar da gabata a garin Kadarko.

Hakazalika jaridar NAIJ.com ta ruwaito cewa, hukumar tsaro ta Kasar Amurka ta cafke wasu 'yan Najeriya 29 da suka aikata laifin zamba da suka saba wawushe dukiyar wasu al'ummar kasar dake gudanar da harkokin kasuwancin su ta yana gizo.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
APC: Muna nan muna neman hanya da wasu Sanatocin PDP don tsige Saraki

APC: Muna nan muna neman hanya da wasu Sanatocin PDP don tsige Saraki

APC: Muna nan muna neman hanya da wasu Sanatocin PDP don tsige Saraki
NAIJ.com
Mailfire view pixel