Kalar abubuwa 7 da suke bawa Hanta matsala, na 7 mutane da yawa na sha

Kalar abubuwa 7 da suke bawa Hanta matsala, na 7 mutane da yawa na sha

- Kafin sanin kalar abincin dake bawa Hantar bil Adama matsala ya kamata mu fara tunatar da masu karatu amfanin Hanta a jikin ɗan Adam da kuma yadda take aiki

- Babbabn aikin Hanta da yawancin mutane suka fi sani shi ne tacewa tare da kore duk wani abu mai guba daga cikin jinin a cikin ɗan Adam

- Haka zalika tana kuma tara rarar sukarin da ta fitar daga abinci ta markaɗa shi sannan ta ajiye shi dumin amfani da shi wajen taimakawa sinadaran cikin jini. Sannan takan kora kwayoyin cutar da ka iya cutar da jiki

Bincike ya nuna cewa Hantar ɗan Adam tana aiki daban-daban sama da 500 domin dai gangar jiki ta zauna lafiya.

Kalar abubuwa 7 da suke bawa Hanta matsala, na 7 mutane da yawa na sha
Kalar abubuwa 7 da suke bawa Hanta matsala, na 7 mutane da yawa na sha

Amma idan hantar mutum ta fara samun matsala, wasu alamomi irinsu tashin zuciya ko kwarnafi, amai da gudawa da kuma rashin ɗanɗano a baki da sauransu ka iya bayyana.

Idan bayan bayyanar waɗannan alamom mutum bai samu kulawar da ta dace ba, manyan alamomi zasu biyu baya irinsu; matsala a tunani (kwakwalwa) ruftawar dubura da kuma nason jini. Wasu lokutan idan abin yayi tsanani mutum ka iya shiga cikin halin rai kwakwai-mutu-kwakwi koma ya sheka barzahu.

1 - Sukari

Kalar abubuwa 7 da suke bawa Hanta matsala, na 7 mutane da yawa na sha
Kalar abubuwa 7 da suke bawa Hanta matsala, na 7 mutane da yawa na sha

Yawaitar shan suga na bawa haƙora matsala haka kuma ita ma hanta bai barta a baya ba, domin yawaitar sukarin a jiki musamman wanda aka sarrafa daga kamfani, yakan tattaro kibar da zata bawa hartar matsala.

Bincike ya nuna cewa irin wannan sukari kanyi kwatankwacin illar da giya take yiwa hanta koda kuwa mutumin ba shi da kiba sosai ba.

KU KARANTA: Karfin fitar da mai ya ragu a wannan watan, hakan na nufin lalitar gwamnati zata yi kasa

A saboda haka ne masana suka shawarci mutane da su rage ta’ammali da alawa mai mutukar zaki da cincin ko duk wani nau’in abinda aka soya ko gasawa da fulawa mai sukari da yawa da kuma lemon kwalba masu zaki da yawa.

2 - Kwaya ko maganin da suka maye gurbin sinadarin Vitamin A

Kalar abubuwa 7 da suke bawa Hanta matsala, na 7 mutane da yawa na sha
Kalar abubuwa 7 da suke bawa Hanta matsala, na 7 mutane da yawa na sha

Vitamin A na da mutukar muhimmanci ga jikin bin Adam, kuma ana samunsa ne ta hanyar cin’ya’yan itatuwa masu kyau da ganyayyaki musamman wadanda suke nau’in kalar ja ko kore da ruwan dorawa.

Saboda cigaban zamani da kuma rashin samun su Vitamin A ko kuma tsada da kayan marmari da na ganyayyakin su keyi a wasu lokutan, sai aka samar da wasu magunguna na ruwa da kuma kwayoyi da suke aiki a jiki kwatankwacinsu.

Sai dai kuma yawaita shan irin wadannan magunguna ka iya haifar da illa ga hanta, saboda haka kafin shansu sai a tuntubi likita.

3 - Lemon kwalba (Soft Drinks)

Kalar abubuwa 7 da suke bawa Hanta matsala, na 7 mutane da yawa na sha
Kalar abubuwa 7 da suke bawa Hanta matsala, na 7 mutane da yawa na sha

Bincike ya nuna cewa duk masu yawaita shan lemon kwalba suna cikin hadarin kamuwa da kibar nan dake haifar da matsala ga hanta (Non-alcoholic fatty liver disease (NAFLD). A shawarce shan kayan marmari ko laimunan da aka yi su daga ‘ya’yan itatuwa shi ne ya fi ga lafiya dan Adam.

4 - Sarrafaffen Kitse (Trans Fats)

Kalar abubuwa 7 da suke bawa Hanta matsala, na 7 mutane da yawa na sha
Kalar abubuwa 7 da suke bawa Hanta matsala, na 7 mutane da yawa na sha

Wannan wani irin sinadari ne da kamfanunuwa kan sarrafa a cikin abinci ko abin sha kamar bota (Butter), yawancinsu a hankali yake taruwa kafin daga bisani yayi yawa a jiki, shi ma yakan haifar da matsala ga hanta a kwana a tashi.

5 - Giya

Kalar abubuwa 7 da suke bawa Hanta matsala, na 7 mutane da yawa na sha
Kalar abubuwa 7 da suke bawa Hanta matsala, na 7 mutane da yawa na sha

Kamru uwar laifi shi ne kirarin da ake yi mata, baya ga tumbele da gusar da hankali da take sawa dadin-dadawa tana muzgunawa wannan sashin jiki mai muhimmanci wato hanta.

Saboda aikin hanta ne wankewa da fitar da duk datti da kuma guba, shan giya kan ninka mata aiki a sakamakon haka sai tayi saurin gajiya karfinta ya kare domin duk ta karar da shi wajen kokarin wanke dattin giyar.

6 - Sarrafaffen abinci (Fast food)

Kalar abubuwa 7 da suke bawa Hanta matsala, na 7 mutane da yawa na sha
Kalar abubuwa 7 da suke bawa Hanta matsala, na 7 mutane da yawa na sha

Dagaske ne kin bata lokaci don yin girki na da dadi musamman idan mutum ba shi da isasshen lokaci, amma fa a kwana da sanin cewa, yawancin irin wadannan abincin na dauke ne da sinadaren sanya kiba ko zakin da kan iya bawa hanta matsala a kwana a tashi (calories da kuma fatty).

7 - Magunguna dangin Paracetamol (Acetaminophen)

Kalar abubuwa 7 da suke bawa Hanta matsala, na 7 mutane da yawa na sha
Kalar abubuwa 7 da suke bawa Hanta matsala, na 7 mutane da yawa na sha

Jin ciwon kai da ciwon baya ko wata ‘ya mashasshara ya sanya mutane yawaita shan maganin Paracetamol ba tare da sanin irin illar da yake yiwa jikinmu ba, yawaita shan irin wadannan magunguna na kashe gajiya ko ciwo na illata hanta sosai. A don haka sai a tabbatar an duba ka’idojin shan sa ko kuma a tambayi likita kafin amfani da shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel