Kamarin talauci: Rashin kudin jarrabawar WAEC ya sanya wasu matasa fara fashi

Kamarin talauci: Rashin kudin jarrabawar WAEC ya sanya wasu matasa fara fashi

- Wasu matasan barayi sun fara da kafar hagu

- Yunkurin satarsu na farko kuma ba su samu nasara ba 'yan sanda suka damke su

- Amma sun yi rokon afuwa kasancewar sun neman kudin da zasu biya jarrabawa ne

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Imo Dasuki Galandanchi yayi holar wasu matasa biyu masu suna Emmanuel Ewudo da Chinwe Nwaane jiya Talata wadanda ake zarginsu da laifin yunkurin fashi da garkuwa da kuma haurawa mutane.

Kamarin talauci: Rashin kudin makaranta ya sanya wasu matasa fara fashi
Kamarin talauci: Rashin kudin makaranta ya sanya wasu matasa fara fashi

Dasuki ya ce rundunar ‘yan sandan zata gurfanar da matasan biyu gaban kuliya, amma sai dai guda daga ciki ya nemi afuwa sakamakon a cewarsa sun shiga sana’ar ne domin tara kudin da zai biya na jarrabawar kammala sakandire ta WAEC.

Matashin ya ce “Don Allah ku taimaka ku rokar mana ‘yan sanda kar su kashe mu, kudin jarrabawa muke kokarin hadawa”.

Kwamishinan ya shaida cewa matasan sun haura gidan wani mata da miji Chigozie Ohajiogu in Akokwa a karamar hukumar Ideato North ta jihar ta Imo da niyyar yi musu fashi.

KU KARANTA: Kalli mai shari’a Adebukola Banjoko wacce ta yankewa tsoffin gwamnoni 2 masu ji da iko hukuncin zaman gidan kurkuku na shekara 28

Kwarmaton da matar ta yi ne ya sanya matasan guduwa amma suka sake dawowa bayan mintuna 45 amma suka sullubewa kamun jami’an ‘yan sanda da suka kawo sumame don kama su. Hakan ta sanya aka je har makarantarsu aka damko su.

Shi ma ‘dayan matashin Nwaane cewa yayi “Dagaske ne mu dalibai ne, mahaifi na yana kwance a asibiti hakan tasa banda halin biyan kudin jarrabawar, sai na roki aboki na ya raka ni wani wuri. Mun je gidan matar don yi mata fashi amma ba muyi nasara ba.

Kwana tsakani sai aka kama mu, mun san cewa haurwa gidan mutane ba dai-dai ba ne amma. Tsoro muke ji ko kashe mu ‘yan sandan zasu yi”.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel