Amurka, Kanada da Mexico za su karɓi bakuncin Gasar cin Kofin Duniya 2026

Amurka, Kanada da Mexico za su karɓi bakuncin Gasar cin Kofin Duniya 2026

A yayin da ake dab da fara fafata gasar cin kofin duniya a kasar Rasha wadda ita ce kasa mai karɓar bakuncin gasar a wannan shekara ta 2018, rahotanni sun bayyana cewa tuni an kaddamar da kasashen da za a fafata gasar a shekarar 2026.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya bayyana da ta kalato cikin rahoton jaridar AFP, kasar Amurka, Mexico da kuma Kanada su ne suka lashe wannan dama ta samun karɓar bakuncin gasar kofin duniya ta 2026 bayan ta doke kasar Morocco cikin zaben da aka gudanar.

Kasashen 3 dake Nahiyyar Amurka ta Arewa sun samu kuri'u 134 cikin 203, yayin da kasar Morocco ta samu kuri'u 65 kacal a taron hukumar kwallon kafa ta duniya da aka gudanar a birnin Moscow ana jajiberin gasar kwallon kafa ta 2018.

Amurka, Kanada da Mexico za su karɓi bakuncin Gasar cin Kofin Duniya 2026
Amurka, Kanada da Mexico za su karɓi bakuncin Gasar cin Kofin Duniya 2026

Legit.ng ta fahimci cewa, za a sake fafata gasar ne a Nahiyyar Amurka ta Arewa cikin kimanin shekaru 24 da suka gaba da kasar Amurka ta karbi bakuncin gasar a shekarar 1994.

Rahotanni sun bayyana cewa, wakilan hukumar kwallon kafa ta duniya ba su samu wani zaɓi ba face kada kuri'un su ga kasashen na Nahiyyar Amurka ta Arewa sakamakon gine-gine filayen wasanni na zamani da alfarma da kuma ingatattun hanyoyin sufuri dake cikin su.

KARANTA KUMA: Goron Sallah: Gwamna Ganduje zai biya Albashin Watan Yuni ga Ma'aikatan Jihar Kano

Sai dai ba bu shakka kasar ta Morocco dake gabar Arewacin nahiyyar Afirka ba a kyale ta haka ba domin kuwa an ma ta alkawarin fafata gasar kofin duniya na Nahiyyar Turai.

Bugu da kari, akwai yiwuwar kasar Morocco ta gaza wajen kammala gine-ginen filayen wasanni, hanyoyin sufuri da kuma masaukai na baki sakamakon bunkasa gasar da za ayi inda kasashe 48 za su fafata a shekarar 2026 sabanin 32 da suka saba karawa a shekarun baya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel