Haihuwa ba tayi rana ba: An damke wani matashi da ya antayawa mahaifiyarsa ruwan zafi

Haihuwa ba tayi rana ba: An damke wani matashi da ya antayawa mahaifiyarsa ruwan zafi

- An kama wani matashi da ya watsa wa mahaifiyarsa tafasashen ruwa a jihar Neja

- Binciken da hukumar NSCDC su kayi ya nuna cewa yaron ya aikata laifin ne cikin maye

- An kuma gano cewa a baya, ya taba yunkurin halaka mahaifiyarsa ta hanyar daba mata wuka

Jami'an hukumar tsaro ta NSCDC reshen Jihar Neja sun kama wani matashi da ake zargi da watsa wa mahaifiyarsa tafasashen ruwa wanda hakan ya haifar mata ta munanan raunuka a jiki.

Kwamandan hukumar na jihar, Mista Philip Ayuba ne ya bayar da sanarwan a yau Talata a birnin Minna.

Haihuwa ba tayi rana ba: An damke wani matashi da ya antayawa mahaifiyarsa ruwan zafi
Haihuwa ba tayi rana ba: An damke wani matashi da ya antayawa mahaifiyarsa ruwan zafi

KU KARANTA: Duk da kassara magoya bayan Buhari a majalisa, an gano suna kara yawa da karfi

Ya ce bayan tambayoyi da akayi wa wanda ake zargin da ke zaune a Okada Road Minna ya nuna cewa ya aikata wannan ma'ashan ne cikin maye bayan ya sha giya tare da codeine har ma da ganyen wiwi.

"Wanda ake zargin bai nuna alamar nadama game da abinda ya aikata ba saboda yadda ya fadda wa jami'an tsaron cewa shine ya watsa wa mahaifiyarsa tafasashen ruwa.

"An gano cewa a baya, ya yi yunkurin kashe mahaifiyarsa sau biyu ta hanyar buga mata katon dutse a kai da kuma caka mata wuka duk a lokacin da ya ke cikin maye sakamakon shan muggan kwayoyi," inji kwamandan.

Ayuba ya shaidawa manema labarai cewa za'a gurfanar da wanda ake zargin bayan kammala bincike kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel