Kotu ta dakatar da Shari'a don ba Dariye damar Kewayawa Bayan Gida

Kotu ta dakatar da Shari'a don ba Dariye damar Kewayawa Bayan Gida

Kamar yadda wasu kafofin watsa labarai suka bayyana musamman shafin jaridar Premium Times da kamfanin Dillanci Labarai na Najeriya suka ruwaito, mun samu rahoton cewa a yau ne ake gudanar da shari'ar tsohon gwamnan jihar Filato, Sanata Joshua Dariye.

Ana zargin tsohon gwamnan da aikata laifin zambar makudan kudi na kimanin Naira Biliyan 1.162 da ya yi almundahana a yayin da kan kujerar gwamnatin jihar sa ta Filato.

Wani rahoto da sanadin shafin jaridar Daily Trust ya bayyana cewa, Alkali Mai shari'a Adebukola Banjoko, ya dakatar da zartar da hukunci yayin gudanar da shari'ar sa na zaman ta a babbar kotun tarayya dake Birnin Abuja.

Tsohon Gwamnan yayin gudanar da Shari'ar sa a Kotu

Tsohon Gwamnan yayin gudanar da Shari'ar sa a Kotu

Rahotanni sun bayyana cewa, Alkalin ya dakatar da shari'ar sa domin bai wa tsohon Gwamnan Dariye damar kewayawa bayan Gida kamar yadda ya bukata.

KARANTA KUMA: Sai mun Dakatar da duk wata Gudanarwa ta Fadar Shugaban Kasa muddin aka taba Obasanjo - ADC

Wannan lamari ya afku ne yayin da Dariye ya kirawa wani ma'aikacin Kotun da misalin Karfe 10.30 na safiyar yau inda ya yi ma sa raɗar bukatar sa cikin kunne, inda ya kuma mika wannan bukata zuwa ga Alkali Mai Shari'a.

Da misalin karfe 10.35 ne kotun ta dakata da gudanar da Shari'ar domin bai wa tsohon gwamnan dama ta biyan bukatar sa a Bayan Gida, yayin da Alkalin cikin jawaban sa ya shaidawa mahalarta kotun dalilin wannan dakaci.

Jaridar NAIJ.com ta kuma ruwaito cewa, Gwamnan jihar Kebbi Abubakar Bagudu, zai biya Albashin watan Yuni ga Ma'aikatan jihar sa domin samun damar gudanar da shagulgulan Sallah cikin farin ciki da Annashuwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dalilin da ya sanya muke so Buhari ya zarce har bayan 2019 Inji wani Gwamna a Arewa

Dalilin da ya sanya muke so Buhari ya zarce har bayan 2019 Inji wani Gwamna a Arewa

Dalilin da ya sanya muke so Buhari ya zarce har bayan 2019 Inji wani Gwamna a Arewa
NAIJ.com
Mailfire view pixel