Zaben 2019: Jam'iyyar PDP tayi karin haske game da yadda zata fitar da dan takarar shugaban kasa

Zaben 2019: Jam'iyyar PDP tayi karin haske game da yadda zata fitar da dan takarar shugaban kasa

Babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta sake jaddada cewa ita fa har yanzu ba ta bai wa kowa tikitin takarar ta na shugaban kasar Najeriya a shekarar 2019 domin siyasa ce za'a buga sannan a fitar da dan takara.

Babban Sakataren gudanawar jam'iyyar a mataki na kasa Mista Austin Akobundu shine ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ya kuma rabwa manema labarai a garin Abuja.

Zaben 2019: Jam'iyyar PDP tayi karin haske game da yadda zata fitar da dan takarar shugaban kasa
Zaben 2019: Jam'iyyar PDP tayi karin haske game da yadda zata fitar da dan takarar shugaban kasa

KU KARANTA: An gano matsalar da ta samu jirgin Osinbajo

Legit.ng ta samu cewa Mista Austin Akobundu ya kara da cewa dukkan rade-raden da wasu jaridun kasar ke bugawa na cewa jam'iyyar ta riga ta fitar da dan takara karya ne tsagwaron ta.

A wani labarin kuma, Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma mai neman tikitin takarar shugabancin kasar Najeriya a jam'iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya gargadi shugaba Buhari da gwamnatin sa da su guji yi wa kundin tsarin mulkin kasar katsalandan domin moriyar su.

Alhaji Atiku Abubakar dai ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar daga ofishin kamfen din sa domin tunawa da soke zaben ranar 12 ga watan Yuni na shekarar 1993.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel