Abu daya da zaka yi ka zauna lafiya a rayuwar ka – Farfesa Sagay ya shawarci Obasanjo

Abu daya da zaka yi ka zauna lafiya a rayuwar ka – Farfesa Sagay ya shawarci Obasanjo

Shugaban kwamitin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa domin samar da hanyoyin yakar cin hanci da hukunta masu aikata hakan, Farfesa Itse Sagay, ya bayyana cewar ikirarin tsohon shugaban kasa Obasanjo na cewar shugaba Buhari na shirin kama shi ya kulle ba gaskiya ba ne.

A karshen makon da ya gabata ne tsohon shugaba Obasanjo ya yi ikirarin cewar gwamnatin shugaba Buhari na yi masa makarkashiya domin garkame shi a gidan yari har abada.

Da yake hira da jaridar Daily Independent, Sagay, ya bayyana cewar sama ba zata fado ba idan gwamnati ta yanke shawarar bincikar Obasanjo a kan kashe dalar Amurka biliyan $16bn domin samar da wutar lantarki lokacin da yake mulki.

Abu daya da zaka yi ka zauna lafiya a rayuwar ka – Farfesa Sagay ya shawarci Obasanjo
Farfesa Sagay

Sagay ya bayyana cewar babbar kalubalen da Obasanjo ke fuskanta a rayuwar sa shine rashin iya suturta bakin sa tare da raina duk mutumin dake mulkin Najeriya. Kazalika ya kara da cewa Obasanjo ji yake tamkar shine shugaban kasar Najeriya koda yaushe.

DUBA WANNAN: 'Yan nPDP sun gindaya sabbin sharuda kafin komawa teburin sulhu da APC

Maganar cewar gwamnati na shirin kama shi ba gaskiya ba ne, ba zance ba ne da ya kamata ‘yan Najeriya su yarda da shi ba. Nayi matukar mamakin jin wannan kalami daga bakin Obasanjo a matsayin san a tsohon shugaban kasa a mulkin soja da farar hula,” a cewar Sagay.

Sagay ya shawarci Obasanjo day a iya bakin sa domin ya samawa kan sa lafiya da zama lafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel