Ali-zai ga-Ali: Donald Trump da Kim Jong-un sun isa Singapore don tattaunawa

Ali-zai ga-Ali: Donald Trump da Kim Jong-un sun isa Singapore don tattaunawa

Labarin da muke samu daga majiyoyin mu na tabbatar mana da cewa shugabannin kasahsen nan biyu na Amurka Donald Trump da takwaransa na kaar Koriya ta Arewa Kim Jong-un yanzu haka sun isa kasar Singapore domin tattaunawar keke-da-keke da suka shirya yi mai cike da tarihi.

Shi dai Mista Donald Trump kamar yadda muka samu, ya isa kasar ta Singapore ne sa'o'i kadan bayan Mista Kim da tawagarsa sun isa kasar.

Ali-zai ga-Ali: Donald Trump da Kim Jong-un sun isa Singapore don tattaunawa

Ali-zai ga-Ali: Donald Trump da Kim Jong-un sun isa Singapore don tattaunawa

KU KARANTA: Biyu daga cikin gaggan barayin bankuna a Offa sun yi lyar zana

NAIJ.com ta samu cewa haduwar ta su da za su yi dai ita ce irinta ta farko tun kafuwar kasashen biyu.

Ana sa ran dai cewa ranar Talata shugabannin biyu za su yi ganawar mai cike da tarihi da kuma duniya ta dade yana jira a wani tsibirin da ake kira Sentosa na Singapore.

Kasar Amurka dai ta bayyana cewa ta na fatar tattaunawar za ta bude kofa ga tsarin da zai sa Kim Jong-un ya hakura da makaman nukiliya.

Shi kuwa Kim Jong-un ya kasance shugaban Koriya ta Arewa na farko da ya taka kafarsa zuwa Koriya ta Kudu inda ya gana da shugaban kasar Moon Jae-in.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain NAIJ.com HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugabannin hukumomin tsaro sun amsa kiran Osinbajo

Shugabannin hukumomin tsaro sun amsa kiran Osinbajo

Shugabannin hukumomin tsaro sun amsa kiran Osinbajo
NAIJ.com
Mailfire view pixel