Rundunar Sojin 'Kasa ta Sheke wasu 'Yan Ta'adda 5 a Jihar Zamfara

Rundunar Sojin 'Kasa ta Sheke wasu 'Yan Ta'adda 5 a Jihar Zamfara

Dakarun Sojin Kasa na Najeriya sun harbe wasu 'yan baranda biyar yayin wani simame da suka kai yankunan da ta'addanci ya yi kamari a karamar hukumar Maru ta Jihar Zamfara.

Shafin jaridar The Punch na ranar Asabar ya bayyana cewa, Bataliyar Sojin kasa mai take Idon Raini ta kai wani simame cikin kauyukan Danguru, Babandoka da kuma Dansadau a karamar hukumar Maru sakamakon rahotannin 'yan ta'adda dake cin Karen su ba bu babbaka a yankunan.

A cewar hukumar Sojin, ta samu nasarar kawar da 'yan ta'adda uku a yayin wani artabu inda kuma ta tarwatsa sansanan su dake kauyukan na Danguru, Babandoka da kuma Dansadau.

Rahotanni sun bayyana cewa, dakarun sun kuma garzaya zuwa kauyukan Gobirawa da Kwacha daura da Dajin Madaka dake yankin garin Dansadau inda suka yi arangama da wasu 'yan ta'adda biyu tare da kawar da su nan take.

'Yan Baranda 5 sun riga mu Gidan Gaskiya yayin da Rundunar Sojin Kasa ta Kai Simame wasu Sansanai a Jihar Zamfara
'Yan Baranda 5 sun riga mu Gidan Gaskiya yayin da Rundunar Sojin Kasa ta Kai Simame wasu Sansanai a Jihar Zamfara

Legit.ng ta fahimci cewa, Kakakin rundunar Sojin Kasa, Birgediya Janar Texas Chukwu, ya tabbatar da wannan rahoto inda ya ce hukumar za ta ci gaba da gudanar da sintiri a yankunan domin cafke sauran 'yan ta'adda da suka tsere.

Yake cewa, hukumar ta samu nasarar cafke wani babur guda da wayar salula mallakin 'yan ta'addan inda ya kuma nemi mazauna yankunan akan ci gaba da bayar da rahotanni da za su taimaka wajen daukar mataki na gaggawa.

KARANTA KUMA: Osinbajo ya Ziyarci Gwamna Ajimobi a Jihar Oyo, Sun Shige Bayan Labule

A ranar Talatar da ta gabata ne Ministan Tsaro, Mansur Dan -Ali, ya gana da shugaban Kasa Muhammadu Buhari tare da shugabannin tsaro na Kasa dangane da kashe-kashen dake ci gaba da afkuwa a jihar Zamfara da kuma yankin Arewa maso Yammacin Kasar nan.

A yayin ganawar ta su Ministan ya nemi a gaggauta daukar mataki da zai magance wannan barazana da a kullum ta ke ci gaba da ta'azzara ba bu sassautawa.

Ministan ya kuma bayar da suanyen kananan hukumomi na Jihar Zamfara da wannan ta'addanci yafi kamari kamar haka; Anka, Maru, Kaura Namoda da kuma Talata Mafara.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, a ranar Juma'ar da ta gabata ne Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya ziyarci jihar Oyo inda ya gudanar da wata ganawa a bayan Labule tare da Gwamna Abiola Ajimobi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel