Jam'iyyar APC ta yi kira ga shugaba Buhari ya karrama Kudirat Abiola

Jam'iyyar APC ta yi kira ga shugaba Buhari ya karrama Kudirat Abiola

- Jam'iyyar APC ta yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya karrama marigayiya Kudirat Abiola

- An yiwa Kudirat Abiola kisar gilla ne a ranar 4 ga watan Yunin 1996 a bayan ta bayyana goyon bayan ta ga mijinta a matsayinsa na zababen shugaban kasa bayan zaben 1993

- Jam'iyyar ta yaba wa shugaba Muhammadu Buhari kan matakin da ya dauka na karrama marigayi Moshood Abiola

Jam'iyyar APC ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karrama marigayiya Kudirat Moshood Abiola wadda ta rasa rayyuwarta a ranar 4 ga watan Yunin 1996 cikin gwagwarmayar tabbatar da cewa gwamnati ta amince da nasarar da mijinta da ya lashe zaben 1993.

Karramawa ta lambar girma da shugaba Buhari ya yiwa Cif Moshood Kashimawo Abiola da marigayi Cif Gani Fawehinmi SAN ya janyo cece-kuce tsakanin yan Najeriya a kafafen yadda labarai.

APC ta bukaci shugaba Buhari ya karrama Kudirat Abiola
APC ta bukaci shugaba Buhari ya karrama Kudirat Abiola

KU KARANTA: An damke wata mahaifiya da ta kashe jaririn ta a Sakkwato

Premium Times ta ruwaito cewa jam'iyyar ta APC ta kuma yaba wa shugaban kasa bisa niyyar sa na karrama abokin takarar marigayi Abiola, Babagana Kingibe.

APC ta ce wannan matakin ta shugaban kasa Buhari ya kara jadada cewa shi mutum ne mai aikata abinda ya kamata ba tare da nuna banbancin siyasa ko wasu manufofi ba.

A cewar jam'iyyar, "A yayin da muke murna tare da sauran 'yan Najeriya tare da yabawa shugaba Muhammadu Buhari kan ayyana ranar 12 ga watan Yuni a sabuwar ranar demokradiyya da kuma karrama Moshood Abiola da lamba girma ta GCFR, muna kira ga shugaban kasan ya yiwa Kudirat Abiola karamcin ita ma.

"Ta cancanta a karrama ta a matsayinta na wanda ta rasa rayyuwarta don tabbatar da demokradiyya. APC ta yi nuni kan yadda Kudirat ta jagoranci dalibai da mata yan kasuwa da masu kare hakkin bil-adama don samar da mulkin demokradiyya."

A wata labarin, Legit.ng ta ruwaito muku yadda wani lauya Cif Mike Ozekhome ya yi tsokaci kan karramawar da Shugaba Buhari ya yiwa marigayi Abiola.

Ozekhome ya ce idan da mutanen biyu suna raye, ba za su amince da karramawar da shugaban kasan ya yi musu ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel