Gwamnati ta rarraba Kayan Agaji ga Nakasassu da Talakawa a jihar Kebbi

Gwamnati ta rarraba Kayan Agaji ga Nakasassu da Talakawa a jihar Kebbi

Da sanadin shafin kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya mun samu rahoton cewa a ranar Juma'a ta yau ne gwamnatin Jihar Kebbi ta rarraba Kayan agaji na sama da Naira Miliyan 50 ga nakasassu da talakawa dake cikin kananan hukumomi 21 a fadin Jihar.

Babban sakataren cibiyar jin kai da jin dadi ta jihar, Alhaji Nasiru Gwandu, shine ya bayyana hakan yayin rarraba kayan agajin ga wakilan cibiyar na kananan hukumomi 21 a Birnin Kebbi.

Yake cewa, manufar gwamnatin jihar ta rarraba kayan agaji ga macancanta itace kwantar da hankulan su dangane da matsalolin da suke fama na kangin talauci, yanayi na rayuwar da yau da gobe da kuma nakasa.

Gwamnati ta rarraba Kayan Agaji ga Nakasassu da Talakawa a jihar Kebbi
Gwamnati ta rarraba Kayan Agaji ga Nakasassu da Talakawa a jihar Kebbi

Babban Sakataren ya bayyana cewa, wannan rarrabe-rarrabe na kayan agaji ya danganta ne dangane da adadin al'umma dake cikin kowane yanki na kananan hukumomin jihar.

KARANTA KUMA: Karamma Abiola da Mukamin GCFR ya tabbatar da shi ya Lashe Zaben Shugaban Kasa na 1993 - Tinubu

Legit.ng ta fahimci cewa an gudanar da wannan goma ta arziki yayin da gwamnatin jihar ta rarraba tan 100 na Shinkafa da kuma Bandir 3000 na atamfofi.

A yayin haka Babban Sakatare ya ke gargadin wakilan kananan hukumomin wajen gaggauta rarraba kayan agajin ga mabukata inda ya kuma tunatar da su muhimmancin gaskiya da adalci musamman a wannan lokaci mai albarka na watan Ramadana.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel