Gwamnan Jihar Neja, Sani Bello, ya karbi Bashin N3.2bn daga Bankin Zenith

Gwamnan Jihar Neja, Sani Bello, ya karbi Bashin N3.2bn daga Bankin Zenith

Da sanadin shafin jaridar Nigerian Daily mun samu rahoton cewa wani gwamna daya daga cikin gwamnonin jihohin Arewa ya samu amincewar majalisar dokoki ta jihar sa wajen karbo bashin makudan kudade daga shahararren bankin nan na Zenith.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne majalisar dokoki ta jihar Neja ta bayar da amincewar ga bukatar gwamnan jihar, Abubakar Sani Bello, na karbar bashin Naira Biliyan 3.2 daga Bankin Zenith.

Majalisar ta bayar da amincewar ta ne da sanadin kuri'un muryoyin 'yan majalisar na yin na'am ko kishiyar hakan bayan wasikar neman izini da Kakakin majalisar, Ahmad Marafa ya karanta yayin zamanta da ta gudanar a ranar Alhamis din da ta gabata.

Gwamnan Jihar Neja, Sani Bello, ya karbi Bashin N3.2bn daga Bankin Zenith
Gwamnan Jihar Neja, Sani Bello, ya karbi Bashin N3.2bn daga Bankin Zenith

Cikin rubutacciyar wasikar da kakakin Majalisar ya karanta, wannan bashi zai tallafawa kasafin kudin jihar na 2018 wajen gudanar da wasu muhimman ayyuka a fadin ta.

Legit.ng da sanadin shafin na jaridar Daily Nigerian ta fahimci cewa, wannan bashi zai tallafa a muhimman ayyuka a sashen ilimi, noma da kuma raya karkara.

Wasikar ta kuma haskaka cewa, wannan bashi na kunshe da kaso 17 cikin 100 na kudin ruwa wanda za a biya a tsakanin watanni 30 masu gabatowa.

KARANTA KUMA: Mutane 6 sun fada tarkon 'Yan sanda dauke da dauri 211 na Tabar Wiwi a Jihar Sakkwato

Rahotanni sun bayyana cewa, sakamakon tanadi na kundin tsarin mulkin kasa ya sanya Gwamna Bello ya nemi izini majalisar dokoki ta jihar sa dangane da karbar wannan bashi.

Cikin na sa jawaban dan majalisa mai wakilcin karamar hukumar Bosso ta jihar, Malik Madaki, ya bayyana cewa bukatuwar wannan bashi ta zo ne domin bai wa jihar dama ta gudanar da muhimman aikace-aikace.

A yayin haka kuma Madaki ya nemi gwamnan jihar akan tattalin wannan dukiya wajen gudanar da ita ta hanyar da aka nufata domin gujewa fushi na majalisar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel