Ranar 12 ga watan Yuni: Yadda IBB ya soke zaben shugaban kasa na MKO Abiola a shekarar 1993

Ranar 12 ga watan Yuni: Yadda IBB ya soke zaben shugaban kasa na MKO Abiola a shekarar 1993

- Marigayi Cif MKO Abiola na jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) ya lashe zaben shugabancin kasa da akayi a ranar 12 ga watan Yunin shekarar 1993

- Masu sharhi kan siyasa da al'umma da dama suna ganin babu wata zabe a tarihin Najeriya da ta dara wannan sahihanci sai dai tsohon shugaban kasan soji, Ibrahim Badamasi Babangida ya soke zaben

- A shekarar 1994, Abiola ya bayyana kansa a matsayin shugaban kasa hakan yasa gwamnatin Janar Abacha ta garkame shi

- Marigayi MKO Abiola ya rasu a ranar 7 ga watan Yulin 1998 cikin wata yanayi mai daure kai

An haifi marigayi Cif Moshood Kashimawo Olawale Abiola ne a ranar 24 ga watan Augustan shekarar 1937 a garin Abeokuta kuma shine da na 23 a wajen mahaifinsa. Abiola ya fara sayar da itace sannan shi da wasu abokansa suka fara waka ana biyansu kudi wanda ya yi amfani da kudin don biyan kudin makarantarsa ta sakandire a Baptist Boys High School da ke Abeokuta.

Ya shiga siyasa yana da shekaru 19 a duniya inda ya yi rajista da jam'iyyar National Council of Nigeria and the Cameroons (NCNC). A wannan lokacin kuma ya fara aiki a matsayin akawu a Barclays Bank da ke Ibadan. Bayan ya yi ayyuka a wasu wuraren ya garzaya kasar Scotland inda ya yi digiri a fannin Akanta kuma ya kammala da daraja ta farko wato 1st Class.

Ya dawo Najeriya ya yi aiki da kamfanoni da dama kuma ya rike manyan mukamai a gida Najeriya da ma wasu kasashen Afirka. Abiola mutum ne mai kishin kasar sa sosai hakan yasa daga baya ya kafa kamfanoni da yawa tare da bayar da taimako ga marasa galihu wanda hakan yasa ya yi farin jini sosai a tsakanin al'umman kabilai da addinai daban-daban.

Ranar 12 ga watan Yuni: Yadda IBB ya soke zaben shugaban kasa da MKO Abiola ya lashe a shekarar 1993
Ranar 12 ga watan Yuni: Yadda IBB ya soke zaben shugaban kasa da MKO Abiola ya lashe a shekarar 1993

DUBA WANNAN: Karramawar da Buhari ya yiwa Abiola da lambar girma ta GCFR ya saba ka'ida - Belgore

Kasancewarsa mai sha'awan siyasa, Abiola ya shiga jam'iyyar National Party of Nigeria (NPN) a shekarar 1980 kuma aka zabe shi ciyaman din jiha ta jam'iyyarsa. An sake yin zabe a jam'iyyar a 1983 kuma shugaban da ya lashe zaben dan jam'iyyar NPN ne hakan yasa Abiola ya kara sanya rai cewa shine zai zama shugaban kasa sai dai kwatsam Soji su kayi juyin mulki a shekarar 1983 wanda hakan ya hambarar da shugaban kasar demokradiyya.

Bayan kimanin shekaru 10 yana mulki, tursasawar da ake yi wa Janar Ibrahim Babangida na mayar da mulki ga farar hula ta yi tasiri. Abiola ya doke Ambasada Baba Gana Kingibe da Atiku Abubakar a zaben sharan fage inda ya zama dan takarar jam'iyyar a zaben 12 ga watan Yunin 1993.

Saboda irin farin jini da ya ke dashi tsakanin al'umma wanda ta ratsa ko ina a Najeriya, kowa a Najeriya ya yi imanin cewa Abiola ne ya lashe zaben shugaban kasa da akayi a 1993 inda ya doke abokin karawarsa, Bashir Tofa na jam'iyyar National Republican Convention (SDP).

Sai dai duk da cewa masu sanya idanu kan zabe na kasa da kasa da al'umman kasa sunyi imanin cewa ba'a taba sahihiyar zabe irin wannan ba a tarihin Najeriya, Shugaban mulkin soji, Ibrahim Badamasi Babangida ya soke zaben ba tare da fadin sakamakon zaben ba inda ya yi ikirarin cewa anyi magudi da rashawa wajen gudanar da zaben. Hakan ya janyo rikice-rikicen siyasa kuma bayan shekara daya Janar Sani Abacha ya yi juyin mulki.

Duk da wannan hayaniya da akeyi, a shekarar 1994 Moshood Abiola ya yi gaban kansa ya ayyana kansa a matsayin halastaccen shugaban kasan Najeriya bayan dawowarsa daga kasashen waje inda ya ke neman hadin kan kasashen don tabbatar masa da nasararsa.

Bayan ayyana kansa a matsayin shugaba kasa, Janar Abacha ya bayar da umurnin a kamo shi bisa laifin cin amanar kasa. An tsare Abiola a kurkuku da tsawon shekaru hudu inda abokan hirarsa kawai sune Kur'ani da Bible sai kuma masu gadinsa guda 14. Shugabanin addinai da shugabanin kasashen duniya sunyi kokarin ganin Abacha ya sake shi amma hakan bai yiwu ba.

Gwamnatin sojin ta ce dole ya janye maganar da ya yi na ayyana kansa a matsayin shugaban kasa amma ya tsaya kan bakansa. Har ma anyi masa alkawarin mayar masa da kudaden da ya kashe wajem kamfe.

Abiola ya rasu jim kadan bayan rasuwar Janar Abacha a ranar 7 ga watan Yulin 1998 da ake shirin sako shi a wata yanayi da mutane ke ganin kashe shi akayi duk da cewa binciken da gwamnati ta fitar ya nuna cewa ba kashe shi akayi ba. Babban jami'in tsaron Abacha, Manjo Al-Mustapha ya yi ikirarin cewa yana da faifan bidiyo da zai nuna cewa duka akayi wa Abiola har ya mutu.

Bayan mutuwarsa, anyi ta yi masa karramawa da bashi lambobin yabo kuma gwamnatin jihar Legas da Ogun tuni sun tsayar da rannan 12 ga watan Yuni a matsayin hutu don tunawa da shi. A jiya shima shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da canja ranar demokradiyya zuwa 12 ga watan Yunin da karrama marigayin tare da bashi lambar karramawa mafi daraja a Najeriya ta GCFR.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel