Dambarwar siyasa: Yarbawa sun goyi bayan majalisar tarayya ta tsige Buhari

Dambarwar siyasa: Yarbawa sun goyi bayan majalisar tarayya ta tsige Buhari

Fitacciyar kungiyar nan ta hadakar 'yan kabilar Yarbawa a Najeriya da aka fi sani da Oodua People’s Congress (OPC) a ranar Talatar da ta gabata ta bayyana jin dadin ta tare da cikakken goyon bayan ta ga majalisar tarayyar Najeriya game da kudurin ta na tsige shugaba Muhammadu Buhari.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun shugaban kungiyar mai suna Frederick Fasehun wanda kuma majiyar mu ta samu inda a ciki ya bayyana cewa hakan ya zama dole idan dai har ana son demokradiyyar mu ta dore.

Dambarwar siyasa: Yarbawa sun goyi bayan majalisar tarayya ta tsige Buhari

Dambarwar siyasa: Yarbawa sun goyi bayan majalisar tarayya ta tsige Buhari

KU KARANTA: Mata za su fara tuki a Saudiyya

NAIJ.com ta samu cewa haka ma dai Mista Frederick Fasehun ya bayyana cewa a yadda kasar ke tafiya dai na nuni ne da cewa shugaban kasar bai koyi wani darasi ba daga dalilan da suka sa aka tsige shi a shekarun baya.

A wani labarin kuma, Shugaban babban ofishin shiyya na hukumar da ke yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) dake garin Fatakwal na jihar Ribas, Nnaghe Itam ya gargadi al'ummar Najeriya da su bi a hankali da 'yan damfara.

Mista Nnaghe Itam ya bayyana cewar kiran ya zama dole ne ganin yadda wasu bata gari ke zuwa suna yin badda-kama suna yaudarar mutane musamman masu hannu-da-shuni cewar wai su za su samar masu da kwangila a ma'aikatar rayawa da cigaban yankin Neja Delta watau Niger Delta Development Commission (NDDC).

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain NAIJ.com HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Girma ya karu: An yiwa El-Rufa'i sarauta

Girma ya karu: An yiwa El-Rufa'i sarauta

Girma ya karu: An yiwa El-Rufa'i sarauta
NAIJ.com
Mailfire view pixel