Cristiano Ronaldo har ya zaɓi Lambar da zai goya a Manchester United - Rahoto

Cristiano Ronaldo har ya zaɓi Lambar da zai goya a Manchester United - Rahoto

Wani rahoto mai yankan kauna da shafin jaridar Daily Trust ta ruwaito ya bayyana cewa, fitaccen dan wasan kwallon kafar nan watau Cristiano Ronaldo, tuni ya zaɓi Lambar da zai goya idan ya koma kungiyar kwallon kafa ta Manchester United.

A cewar Don Balon, wata kafar watsa labarai a can kasar Andalus watau Spain, Ronaldo ya bukaci goya sananniyar lambar da ya saba goyawa watau Lamba 7.

Cristiano wanda ya goya wannan Lamba har na tsawon shekaru shidda a Manchester United kafin ya koma Kungiyar Kwallon kafa ta Real Madrid a shekarar 2009 ya sake bayyana muradin sa akan wannan Lamba.

Sai dai hanzari ba gudu ba, fitaccen dan wasan nan da Manchester United ta sayo daga Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal watau Alexis Sanchez, shike sanye da wannan Lamba tun watan Janairun da ya gabata.

Cristiano Ronaldo har ya zaɓi Lambar da zai goya a Manchester United - Rahoto
Cristiano Ronaldo har ya zaɓi Lambar da zai goya a Manchester United - Rahoto

Jaridar ta Don Balon ta yi ikirarin cewa, babban mai horas da yan wasa a kungiyar Manchester United, Jose Mourinho, ya bayyana cewa dole Sanchez ya mika wannan Lamba ga Ronaldo matukar yana son zaman sa a kungiyar.

KARANTA KUMA: Gwamnatin Tarayya ta tsawaita izinin Hutun Haihuwa zuwa Watanni 4 a Najeriya

Rahotanni sun bayyana cewa, zabi dai a halin yanzu ya rage ga Sanchez dan asalin Kasar Chile na hakura da wannan Lamba ko kuma ya kama gaban sa wajen neman wata sabuwar Kungiyar.

Legit.ng ta fahimci cewa, tuni dai hasashe ya bayyana cewa Cristiano Ronaldo na neman barin farfajiyar wasanni ta Santiago Bernabue inda yake baje basirar sa ta tamola a kungiyyar kwallon kafa ta Real Madrid.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel