Shugaba Buhari da Ministocin sa sun yi Bankwana da Fayemi yayin Zaman Majalisa

Shugaba Buhari da Ministocin sa sun yi Bankwana da Fayemi yayin Zaman Majalisa

A ranar yau ta Laraba ne shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da Ministocin sa, suka yi bankwana ga Ministan tattalin ma'adanan Kasa, Kayode Fayemi, a sakamakon murabus da yayi a domin tsayawa takarar kujerar gwamna ta jihar Ekiti da za a gudanar a ranar 14 ga watan Yuli.

Shugaba Buhari cikin jawaban sa na bankwana gabanin fara gudanar da zaman majalisa ya godiya gami da yabo ga tsohon Ministan sakamakon muhimmiyar rawar gani da ya taka a gwamnatin sa wajen kawo ci gaba musamman a ma'aikatar sa ta ma'adanan Kasa.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, an zabi 'yan Majalisar shugaba Buhari guda shidda daga sassa daban-daban na fadin Kasar nan domin gabatar da jawaban su na bankwana ga tsohon Ministan.

Shugaba Buhari da Ministocin sa sun yi Bankwana da Fayemi yayin Zaman Majalisa

Shugaba Buhari da Ministocin sa sun yi Bankwana da Fayemi yayin Zaman Majalisa

Shugaba Buhari da Ministocin sa sun yi Bankwana da Fayemi yayin Zaman Majalisa

Shugaba Buhari da Ministocin sa sun yi Bankwana da Fayemi yayin Zaman Majalisa

NAIJ.com ta fahimci cewa, Ministocin da suka gabatar da jawaban su na bankwana masu tattare da tarin yabo gami da jinjina ga tsohon Ministan sun hadar da; Ministan ma'aikatar Kimiyya da Fasaha Ogbonnaya Onu da Ministan harkokin cikin gida Abdulrahman Dambazau.

KARANTA KUMA: Ba bu Hannun Osinbajo wajen bayar da Umarnin Sallamar Ma'aikaciyar Amnesty - Fadar Shugaban Kasa

Sauran wadanda suka tofa albarkacin bakin su sun hadar da; Ministar Mata Amina Alhassan, Ministan Kudi Kemi Adeosun, Ministan Sufuri Rotimi Amaechi da kuma Karamin Ministan ma'adanan Kasa, Bawa Bwari.

Rahotanni sun bayyana cewa, Ministocin sun kyautata tsammanin su akan Fayemi dangane da ceto jihar Ekiti daga cikin kangin da jam'iyyar adawa ta PDP ta jefa ta a ciki.

A yayin haka kuma, shugaba Buhari ya sake janyo hankalin 'yan Majalisar sa wajen wayar da kawunan al'ummar Najeriya dangane da sanin muhimmancin katin zabe inda yake cewa shi kadai ne zai kwato 'yancin su a Kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Wani miji ya silale cikin asibiti kawai domin tarawa da matarshi mai jinya

Wani miji ya silale cikin asibiti kawai domin tarawa da matarshi mai jinya

Wani miji ya silale cikin asibiti kawai domin tarawa da matarshi mai jinya
NAIJ.com
Mailfire view pixel