Shugaban Kasa Buhari ya nada Alkalin Alkalai na babban Kotun Tarayya

Shugaban Kasa Buhari ya nada Alkalin Alkalai na babban Kotun Tarayya

- Shugaba Buhari ya nada Abdul Kafarati a matsayin Alkalin Alkalai

- Alkalki Kafarati zai cigaba da shugabantar babban Kotun Tarayya

- Amma dai sai Majalisar Dattawa ta amince da wannan nadi tukuna

Mun samu labari cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada Alkalin Alkalai na babban Kotun Tarayya a makon nan. Majalisar Dattawan Kasar ta tabbatar da wannan a zaman da tayi a jiya Talata da rana.

Shugaban Kasa Buhari ya nada Alkalin Alkalai na babban Kotun Tarayya
Buhari ya nada Abdul Kafarati a matsayin Alkalin Alkalai

Shugaban Kasar ya nada Alkali mai shari’a Adamu Kafarati a matsayin Shugaban Alkalan babban Kotun Tarayyar Najeriya kamar yadda Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya bayyana a gaban Majalisa inda ya karanto takardar Shugaban kasar.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya sha ruwa tare da Manyan Kasa

Yanzu dai dole sai Sanatocin Kasar sun tantance Alkali Abdul Adamu Kafarati a kafin ya zama takamaiman Alkalin Alkalai na babban Kotun Kasar. Shugaba Buhari dai yana sa rai Majalisar Dattawan ta amince da wannan mukami da ya bada.

Kafin nan dai Abdul Adamu Kafarati shi ne Mukaddashin Alkalin Alkalai na Kotun inda yake rikon kwarya. Wannan karo Shugaban Kasa Buhari ya nemi Majalisa ta tabbatar da shi a kan wannan matsayi kamar yadda tsarin dokar kasa ta tanada.

A makon nan dai ne wani rikici yake kokarin barkewa tsakanin Shugaban Kasa Buhari da Majalisa inda ‘Yan Majalisar Wakilai da ta Dattawa su ka sha alwashin tsige Shugaba Muhammadu Buhari a dalilin binciken da ake yi kan wasu manya a Majalisar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel