Babu wanda ya isa ya tsige Buhari matukar ina raye – Inji Gudaji Kazaure

Babu wanda ya isa ya tsige Buhari matukar ina raye – Inji Gudaji Kazaure

Shahararren masoyin shugaban kasa Muhammadu Buhari, dan majalisa Muhammadu Gudaji Kazaure ya bara game da kutun kutun da kafatanin yan majalisun dokokin Najeriya ke shirya ma shugaba Buhari, inda suka yi barazanar tsige shi, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Gudaji yana cewa bau yadda za’a yi a hada baki da shi wajen tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda yace idan har yana da rai babu wanda ya isa ya tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari daga mukaminsa.

KU KARANTA: Ba tsoron Allah: Labarin yadda wasu Musulmai ke karyar azuminsu don abin Duniya

Gudaji ya bayyana haka ne a wani taron manema labaru da ya shirya jim kadan bayan kammala taron yan majalisun da suka yi, inda a bayan taron suka gindaya ma Buhari wasu sharudda 12, idan bai cikasu ba zasu tsige shi.

Babu wanda ya isa ya tsige Buhari matukar ina raye – Inji Gudaji Kazaure
Gudaji Kazaure

“Babu wanda zai tsige Buhari matukar ina numfashi a majalisa, za ayi yaki idan aka kuskura aka nemi a tsige Buhari.” Inji Honorabul Gudaji Kazaure. Sai dai Gudaji yayi kira ga shugaba Buhari da ya shigo cikin rikicin nan don sulhunya tsakani.

“Ina kira ga shugaban kasa da ya shigo cikin matsalar nan don kawo karshenta, kun sani a shekarar 2015 bamu da kudi, bamu da gwmanati, amma kuma babu wanda yayi mana barazana, a haka Allah ya bamu mulki, don haka bai kamata gwamati ta yi ma wasu barazana ba saboda zaben 2019.” Inji shi.

Daga karshe ya shawarci Buhari da ya sulhunta da duk wadanda ya bata dasu a siyasance, yace babu dadi ace mutanen da suka sha wahala da Buhari tun a shekarar 2003 sun zama yan kallo a gwamnatin nan. “Don haka bai kamata ya zura idanu yana kallon wasu yan tsiraru suna raba shi da mutane da ba”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel