Jihohin Najeriya 10 da ke gaba a yawan masana'antu

Jihohin Najeriya 10 da ke gaba a yawan masana'antu

Jihohin da ke da karfin masana'antu sune ke kan gaba wajen samar wa kasa kudaden shiga ta hanyar haraji. Najeriya tana da jihohi 36, cikinsu Legit.ng Hausa za ta kawo muku wadanda suke kan gaba wajen samarwa baitil malin Najeriya kudi.

Jihohi 10 da su kafi cigaba a fannin masana'antu a Najeriya
Jihohi 10 da su kafi cigaba a fannin masana'antu a Najeriya

10. Jihar Kaduna

Jihar Kaduna cibiyar ilimi ne kuma jihar ta hada wasu jihohi da dama wanda suke cinikayya da juna.

Akwai masana'antu kamar na tufafi da karafa da man fetur da sauransu. Harkan kere-kere na kasa shima yana cin kasuwar shi musamman daga mutane kabilar Nok.

Noma itace abinda galibin mutanen jihar su kafi dogara a kai. Suna noman auduga, Coacoa, gyada, doya, masara. cita, shinkafa, rogo, gero, dawa da sauransu.

Ana noma sama da ton 180,000 na gyada a jihar a duk shekara kuma akan fitar da wasu kayayakin abincin kasashen waje.

Akwai masana'atun taki, flawa, kirar mota (Peugeot), wayan wuta da sauransu.

09. Jihar Osun

Jihar Osun tana daya daga cikin yankunan da masana'antun sarafa sinadaren Chemical suka fi yawa a Najeriya. Suna da masana'antu masu dimbin yawa. Masan'antun da suka shara a jihar sun hada da Samtop Paint Chemical Industries, Criss Cross Integrated Services, Webring Integrated Services Limited da sauransu.

Fannin da ake sa ran zai fi bunkasa nan gaba shine masana'antar sarrafa Cocoa wanda suke samar da fiye da ton 20,000 a kowacce rana.

08. Jihar Akwa Ibom

Jihar na da adadin mutane kimanin 5 miliyan. Akwa Ibom ce jihar ta farko da ta fara amfani da kamfanin kera na'aurar mita na lantarki. An bula da shi ne don rage tsadar lantarki.

Jihar na da masana'antun sarrafa sinadaren Chemicals da yawa. Suna da kamfanin kera Pencil da tsinken sakuce. Har ila yau, Jihar na daya daga cikin jihohin masa samar da man fetur da iskar gas.

07. Jihar Kano

Jihar Kano ce ke kan gaba a fannin masana'antu a Arewa. A yanzu jihar na sa sama da masana'antu 100 masa sarrafa abubuwa daban-daban. Masan'antun sun hada da na sarrafa abincin dabobi, madara, man gyada, abinci, lemun kwalba, magunguna, takalma, tufafi, sarrafa fata, kayan shafa da sauransu.

06. Jihar Oyo

Wannan jihar ce ke da babban kamfanin sarrafa tabar cigari a Najeriya. Akwai wuraren saka jari sosai kuma kasar na kan gaba wajen ayyukan noma a Najeriya.

05. Jihar Abia

Daya faga cikin manyan masana'antun da ake jihar shine na man fetur da iskar gas. A halin yanzu jihar ya samar da 2% na kudin shiga a Najeriya.

Babban birnin da masana'antu su kafi yawa shine Aba. Akwai kamfanoni da dama kamar na kera takalma, sabulu, magunguna, tufafi, siminti da sauransu. Kimanin 70% na mutanen jihar suna aiki ne a fanin noma.

04. Jihar Anambra

Jihar na daya daga cikin jihohin da ke kan gaba wajen samar da man fetur a Najeriya, suna da ma'adinai da dama da suka hada da bauxite, man fetur da iskar gas da sauransu. Jihar ne ke da matatan mai mai zaman kanta mafi girma a Najeriya, Orient Petroluem.

03. Jihar Ogun

Ogun tana kudu maso yammacin Najeriya ne kuma akwai masana'antu masu yawa sosai a jihar masu sarrafa abinci, tufafi, lemun kwalba da sauransu. Jihar na guraben saka jari sosai.

02. Jihar Rivers

Rivers na daya daga cikin jihohin da ke kan gaba wajen samar wa Najeriya kudin shiga. Jihar na da man fetur da iskar gas.

Jihar na samar wa Najeriya 60% na danyen man fetur. Fannin makamashi ne ke kan gaba wajen samarwa mutane aiki. Jihar tafi dukkan sauran jihohin Najeriya amfani da lantarki hakan yasa mahukuntar jihar ke kokarin samar da lantarki na hasken rana.

01. Jihar Legas

Legas ce cibiyar kasuwanci da cinikayya a Najeriya hakan yasa itace jihar da tafi kowanne yawan masana'antu a Najeriya. Kazalika, Legas ne cibiyar harkokin sadarwan zamani da kirkire-kirkire a Najeriya.

Wadannan jihohin da aka lissafo sune ke kan gaba wajen samarwa Najeriya kudaden shiga. Najeriya kuma tana daya daga cikin kasashen da ke da yawan masana'antu a Afirka kuma masana sunyi hasashen za'a samu cigaba sosai muddin gwamnati ta samar da yanayi mai kyau.

KU KARANTA: Talauci ya sanya na sayar da jariri na kan kudi N670,000 - Wata matashiya 'yar shekaru 17

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel