Bi-ta-da-kulli: Hukumar EFCC sake kama hadimin Kanal Dasuki bisa zargin handamar Naira biliyan 3

Bi-ta-da-kulli: Hukumar EFCC sake kama hadimin Kanal Dasuki bisa zargin handamar Naira biliyan 3

Hukumar nan dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) a ranar Litinin din da ta gabata 4 ga watan Yuni ta sake gurfarar da Kanal Nicholas Ashinze, tsohon hadimin Kanal Dasuki a gaban kotu.

Kamar yadda muka samu, EFCC din sun gurfanar da shi ne tare da wasu mutane uku ne bisa zargin handame wasu kudaden jama'a da suka kai Naira biliyan 3.6.

Bi-ta-da-kulli: Hukumar EFCC sake kama hadimin Kanal Dasuki bisa zargin handamar Naira biliyan 3

Bi-ta-da-kulli: Hukumar EFCC sake kama hadimin Kanal Dasuki bisa zargin handamar Naira biliyan 3

KU KARANTA: Cigaba da tsare Zakzaky rashin adalci ne - Buba Galadima

NAIJ.com ta samu cewa EFCC din dai ta gurfanar da su ne a gaban babbar kotun tarayya dake zamanta a unguwar Maitama a can garin Abuja, babban birnin tarayya.

A wani labarin kuma, Kamar yadda muke samun labari daga majiyoyin mu, alkalin wani babbar kotu a jihar Oyo Mai shari'a ML Owolabi ya ranar Litinin din da ta gaba ya yi mursisi ya hana bukatar da tsohon gwamnan jihar Otunba Adebayo Christopher Alao-Akala ya shigar a gabanta bisa ga shari'ar da yakeyi da hukumar EFCC.

Shi dai tsohon gwamnan, kamar yadda muka samu, ya shigar da wata kara ce a gaban kotun koli ta kasa yana kalubalantar shari'ar da ake yi masa kuma yanzu haka yana jiran tsammanin hukunci daga gare su.

dan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain NAIJ.com HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sallar idi: Sanata Rabiu Kwankwaso yayi sallah a Kudancin Najeriya

Sallar idi: Sanata Rabiu Kwankwaso yayi sallah a Kudancin Najeriya

Tsohon Gwamnan Kano Kwankwaso yayi sallah a Jihar Edo
NAIJ.com
Mailfire view pixel