Ana yiwa Ramos barazana bisa raunin da yayi wa Salah

Ana yiwa Ramos barazana bisa raunin da yayi wa Salah

Majiya mai karfi daga kasar Spain ta bayyana cewar fitaccen dan wasan kungiyar kwallon kafan nan ta Real Madrid, Sergio Ramos ya canja layukan wayarsa tare dana matarsa, saboda kiran waya da sakonni da suke karba wanda ake ta faman yi musu barazanar cewar za'a ga bayan su

Ana yiwa Ramos barazanar kisa
Ana yiwa Ramos barazanar kisa

Majiya mai karfi daga kasar Spain ta bayyana cewar fitaccen dan wasan kungiyar kwallon kafan nan ta Real Madrid, Sergio Ramos ya canja layukan wayarsa tare dana matarsa, saboda kiran waya da sakonni da suke karba wanda ake ta faman yi musu barazanar cewar za'a ga bayan su.

DUBA WANNAN: Zargin aikata zina a watan Ramadan yasa sunyi mata dukan kawo wuka

Sergio Ramos dai shine wanda ya jiwa shahararren dan kungiyar kwallon kafan nan ta Liverpool, wato Muhammad Salah mummunan ciwo a kafadar shi a wasansu na karshe na cin kofin zakarun turai wanda suka buga a watan daya gabata a kasar Ukraine, tsakanin kungiyar Real Madrid da Liverpool, inda madrid suka cinye wasan.

Rahoto daga kasar ta Spain sun bayyana cewar Ramos da matarsa suna samun karbar sakonn a wayoyin su na salula da ake yi musu barazanar cewa za'a kashe su saboda ciwon da Ramos din ya jiwa Salah a kafada, wanda a yanzu haka ake tunanin cewar Salah din bazai samu damar buga wasan su na farko ba na cin gasar kofin duniya.

Hukumar 'yan sanda ta kasar Spain sun samu rahoto akan lamarin na Ramos inda tuni suka fara baza bincike akan lamarin, kuma sunyi barazanar cewa duk wanda hukumar ta samu da laifin aika sakon barazanar kisa zuwa ga wayar Ramos ko matar sa to tabbas akwai hukunci mai tsanani.

Hukumar kwallon kafa ta kasar Egypt ta sanar da cewa Salah zai dawo nan bada dadewa ba kuma zai buga gasar cin kofin duniya, sai dai kuma da wuya ace ya buga wasan farko da zasu kara da kasar Uruguay.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel