Yanzu Yanzu: Rundunar yan sanda ta soke sammacin da ta aikewa Saraki, ta gabatar da sabon bukata a gare shi

Yanzu Yanzu: Rundunar yan sanda ta soke sammacin da ta aikewa Saraki, ta gabatar da sabon bukata a gare shi

Rundunar yan sandan Najeriya ta soke sammacin da ta aikewa shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki inda da farko bukaci ya gurfana a gabanta bayan an zarge shi da nasaba da fashin bankin Offa.

Shugaban majalisar dattawan ta shafinsa na twitter a ranar Litinin, 4 ga watan Yuni yayi bayanin cewa rundunar yan sandan ta bukaci ya amsa mata ta sakon rubutu.

Saraki yace yana shirin yin hakan.

Ya rubuta: “Bayan sakon farko da na wallafa ashafin twitter, na samu sako daga @PoliceNG. Sun janye cewar na gurafana a gaban ko wani ofishinsu, sai dai cewar na basu amsa ta sakon wasika kan zargin cikin sa’o’i 14 – Wanda nake shirin yi.”

KU KARANTA KUMA: Lauretta ta bayyana Buhari, Obasanjo da IBB a matsayin nagari, mugu da mummuna

Hakan na zuwa ne yan sa’o’i kadan bayan Saraki yace bai samu ko wani sakon gayyata daga yan sanda ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnonin Najeriya 5 da suka fi yiwa jama’ar su aiki da bangaren da kowanne yafi dagewa, za a karrama su

Gwamnonin Najeriya 5 da suka fi yiwa jama’ar su aiki da bangaren da kowanne yafi dagewa, za a karrama su

Za a karrama gwamnoni 5 da suka fi yiwa jama’a aiki, duba bangaren da kowanne yafi dagewa
NAIJ.com
Mailfire view pixel