Yan biyun da ke rayuwa a hade sun mutu suna da shekaru 21 a duniya

Yan biyun da ke rayuwa a hade sun mutu suna da shekaru 21 a duniya

Duniya budurwar wawa! Kasar Tanzania na cikin jimami na babban rashin da suka yi na tagwayen nan da ke rayuwa a hade da suka shiga zran jama'ar kasar wato Maria da Consolata Mwakikuti.

Tagwayen sun rasu ne suna da shekara 21 a sanadiyar matsalar numfashi da suka samu.

Yan biyun na sarrafa wasu sassa na jiki kamar hanta da huhu tare , amma kuma suna da zuciya biyu, Haka zalika kwunansu a rabe yake zuwa kafada.

Sun fara jinya ne a karshen shekarar da ta gabata bayan sun samu matsalar da ta shafi numfashi, sun kuma rasu a ranar Asabar din da ta gabata.

An rahoto cewa mahaifiyar yaran ta rasu bayan haihuwarsu sannan kuma ba’a jima ba mahaifinsu ya bi ta inda suka zama cikakkun marayu.

Yan biyun da ke rayuwa a hade sun mutu suna da shekaru 21 a duniya

Yan biyun da ke rayuwa a hade sun mutu suna da shekaru 21 a duniya

KU KARANTA KUMA: Jarrabawar shiga jami’a: Nayo hayar wani ne saboda ‘dana – Uwa ta tona asiri

Wani cocin Katolika mai suna Maria Consolata ne ta dauki naiuyinsu, inda aka sanya masu sunan cocin.

Burin yaran shine su zamo malaman makaranta bayan sun kammala karatunsu.

Idan ka na da korafi ko shawara, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku bidemu a shafukanmu https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dino Melaye ya kai kukansa ga Buhari game da yunkurin da ake yi na halaka shi

Dino Melaye ya kai kukansa ga Buhari game da yunkurin da ake yi na halaka shi

Magiya: Ka shiga tsakanina da masu neman halaka ni – Dino Melaye ga Buhari
NAIJ.com
Mailfire view pixel