Wata ma'aikaciyar gwamnati ta rasa aikinta bayan sukar Osinbajo da Aisha Buhari

Wata ma'aikaciyar gwamnati ta rasa aikinta bayan sukar Osinbajo da Aisha Buhari

Wata mace 'yar Najeriya, Bolouere Opukiri ta rasa aikin ta mako daya bayan ta yi suka a kan mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha a dandalin sada zumunta na Twitter.

A ranar 5 ga watan Yulin shekarar 2017, Opukiri da ayyana cewa Osinbajo 'Dan koyo' ne saboda ya yi tafiya zuwa kasar waje a yayinda shugaba Buhari ke birnin Landan duk da cewa ana samun rashin jituwa tsakanin fadar shugaban kasa da majalisa a wannan lokacin.

KU KARANTA: Dubi yadda jihohin Arewa ke kan gaba wajen adadin mutanen da za'a dauka aikin 'Dan sanda

Wasu Sanatocin Najeriya sunyi suka a kan tafiyar na Osinbajo kwana daya kafin matar tayi nata sukar, Sanata Enyinnaya Abaribe na jihar Abia ya ce tafiyar ta Osinbajo ta bar wani 'gibi' da ya dace shugaban majalisa Bukola Saraki ya cike ta.

Wata mata ta rasa aikinta bayan sukar Osinbajo da Aisha Buhari
Wata mata ta rasa aikinta bayan sukar Osinbajo da Aisha Buhari

Kazalika, ta kuma sake yin wani rubutu a Twitter kwanaki biyar bayan na farkon inda ta soki Aisha Buhari da cewa ta fiye kwakwazo a kan wasu daga cikin 'kuraye' da 'dila' da kusanci da mijinta inda ta ke kokarin nuna cewa Aisha Buhari ba da da wayewa irin ta tsohuwar matar shugaba Jonathan wato Patience.

Wata mata ta rasa aikinta bayan sukar Osinbajo da Aisha Buhari
Wata mata ta rasa aikinta bayan sukar Osinbajo da Aisha Buhari

Wasu 'yan Najeriya masu kishin gwamnatin Buhari sun tattara wannan rubuce-rubuce guda biyu da ma wasu da suka biyo baya kuma suka aike da shi zuwa ga ofishin yada labarai na shirin yin afuwa ga masu tada kayan bayan Neja Delta inda Opukiri ke aiki don daukan mataki.

Ofishin ta yi nazari a kan rubuce-rubucen tare da yin wasu bincike kuma daga baya ta yanke shawarar korar Ms Opukiri inda suka ce abinda ta yi ya sabawa dokokin aikin gwamnati kuma barazana ce ga tsaron kasa.

Ms Opukiri ta shaida wa Premium Times cewa korar da akayi mata ba bisa ka'ida bane kuma an tauye mata hakkin bayyana ra'ayinta inda ta ce tabbas za ta garzaya kotu don a bi mata hakkin ta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel