Asiri ya sake tonuwa: Wata daliba ta sake tona asirin wani Farfesa da ke neman kwanciya da ita

Asiri ya sake tonuwa: Wata daliba ta sake tona asirin wani Farfesa da ke neman kwanciya da ita

Kimanin wata daya bayan wata dalibar Jami'ar Obafemi Awolowo da ke jihar Osun ta tona asirin wani Farfesa da ke neman kwanciya da ita kafin ya bata makin cin jarabawa, wata dalibar jami'ar Legas (Unilag) ta sake fitowa inda ta ke zargin wani Farfesa da tursasa mata yin lalata da shi.

Malamin jami'an da dalibar ke zargi shine Olusegun Awonusi, Farfesan harshen turanci a jami'ar Legas (UNILAG) kuma tsohon shugaban jami'ar Ilimi na Tai Solarin (TASUED) da ke Ijagun a jihar Ogun.

Dalibar wanda a halin yanzu ta nemi ta nemi a sakaya sunanta ta yi ikirarin cewa tana da hotunan Farfesan yana zigidir. Ta kuma ce Farfesan ya shafe watanni yana tursasata wai sai ta kwanta da shi.

Kuma dai: An sake tona asirin wani Farfesa mai kwanciya da dalibai don maki
Kuma dai: An sake tona asirin wani Farfesa mai kwanciya da dalibai don maki

KU KARANTA: 2019: Zan azurta ku da miliyoyi idan ku ka sake zabe na - Gwamnan wata jihar Arewa

Ga wasu daga cikin kalaman dalibar kamar yadda kafar yadda labarai na Linda Ikeji ya wallafa: "Na shafe watanni ina shan bakar wahala. Duk lokacin da dalibai mata suka shiga ofishinsa, sai ya yi kokarin ya taba su. Na dauki hotonsa cikin kwanakin nan da na shiga ofishinsa. Kowa ya san shi da zagewa mata. Yanzu haka rayuta na cikin hadari a jami'ar nan shiyasa na sanar da ke don a taka masa birki."

Ta kara da cewa: "Farfesa na a sashin nazarin harshen turanci, kuma ba ni bace ta farko da ya ke kokarin zagewa. Hakan ya ke yi wa dukkan dalibai mata. Na rasa yadda zanyi da karatu na saboda ya fadar da ni jarabawarsa a baya. Da na same shi don inji dalilin faruwar hakan sai ya ce min ni ba karamar yarinya ba ce saboda haka na san abinda ya dace inyi. Ina matukar juyayin barin tsohon kamansa ya taba ni amma shi bai damu ba."

Dalibar ta cigaba da cewa ba shi kadai bane ke irin wannan halin wai akwai wasu malamai da yawa da ke yin hakan shi yasa duk suke hada kansu waje guda.

A bangarensu, mahukuntar jam'ar sun dau alwashin gudanar da sahihiyar bincike don gano gaskiyar lamarin kamar yadda suka sanar a ranar 30 ga watan Mayu inda suka shawarci al'umma su kwantar da hankalinsu.

Jami'ar ta tabbatar wa iyayen yara, dalibai, ma'aikata da masu ruwa da tsaki a jami'an cewa ba za'ayi sakwa-sakwa a kan batun ba kuma tana rokon mutane cewa duk wanda ya ke da wani karin bayani a kan zargin ya taimaka a sanar da jami'an ba tare da an fallasa shi ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel