Kama Lamaran Yero: Da ana bin ta laifi ne da Buhari ma bai zama shugaban kasa ba - Sheikh Gumi

Kama Lamaran Yero: Da ana bin ta laifi ne da Buhari ma bai zama shugaban kasa ba - Sheikh Gumi

Babban malamin nan na Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi ya caccaki gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da hukumar yaki da cin hanci da rashawa wato EFCC.

Shehin malamin ya nuna bakin ciki kan yadda aka tozarta tsohon gwamnan jihar Kaduna Lamaran Yaro, inda hukumar EFCC ta ba shi takarda ya rike a matsayin mai laifi.

Ya jadadda cewa da ana bin laifi toh da babu shakka Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai zamo shugaban kasar Najeriya ba. A cewarsa mutane ne kawai suka yafe.

Daga karshe ya kalubalanci shugaban kasar da ya zo a auna shi a sikeli tare da Shagari don aga wa yaci kudin gwamnati a cikinsu.

Kama Lamaran Yero: Da ana bin ta laifi ne da Buhari ma bai zama shugaban kasa ba - Sheikh Gumi

Kama Lamaran Yero: Da ana bin ta laifi ne da Buhari ma bai zama shugaban kasa ba - Sheikh Gumi

Ga yadda ya zo a fadar malamin: “An nuna mun tsohon gwamnan jihar Kaduna Lamaran Yero EFCC sun sa shi ya rike wata takarda wai ita offence wannan kuskure ne, yayi kuskure dole mu fada masa.

KU KARANTA KUMA: Dan majalisar tarayya daga jihar Jigawa ya sha da kyar a hannun masu zanga-zanga

“Kudu fa ta dawo daga rakiyar wannan gwamnati kune kawai dakikan banza.

“Da ana bin laifi ko janar Muhammadu Buhari ba zai zamo shugaban kasa ba Mutane ne suka yafe.

“Shagari babana ne dan uwana ne a zo a sa shi a sikei da Shagari aga wa ya ci kudin gwamnati.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kalli Jaririyar farko da aka haifa a filin Arfa a hajjin bana (hoto)

Kalli Jaririyar farko da aka haifa a filin Arfa a hajjin bana (hoto)

Kalli Jaririyar farko da aka haifa a filin Arfa a hajjin bana (hoto)
NAIJ.com
Mailfire view pixel