Komawa APC ba zai cece ku ba – Fadar shugaban kasa tayi ba’a ga barayin yan siyasa

Komawa APC ba zai cece ku ba – Fadar shugaban kasa tayi ba’a ga barayin yan siyasa

Hadimar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Lauretta Onochie tayi gargadin cewa rungumar jam’iyyar All Progressives Congress, APC, ba zai kare barayin yan siyasa ba.

Lauretta tayi ba’a ga barayin gwamnatin ne a ranar Alhamis, 31 ga watan Mayu.

Da take maida martani akan hukuncin dauri da wata babban kotun tarayya ta yankewa tsohon gwamnan jihar Taraba, Mista Jolly Nyame, a ranar Laraba, Onochie ta yi gargadin cewa hukuncin da akayi masa ya nuna cewa APC ba aljanar masu laifi bane.

Sannan kuma Onochie tayi ba’a ga jam’iyyar PDP a shafin Facebook inda tace sun kasa daure tsohon gwamnan.

KU KARANTA KUMA: Jam’iyyar APC ba za tayi nasara a 2019 ba Inji Gwamna Dickson

Idan zaku tuna a baya NAIJ.com ta tattaro cewa wata babbar kotun tarayya ta yankewa tsohon gwamnan jihar Taraba shekaru 14 a gidan yari ba tare da tara ba.

Hakazalika a yanzu haka an gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ramalan Yero a gaban kotu bayan tuhumar amdame kudi da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ke yi masa tare da wasu yan siyasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Talala: Hukumar EFCC ta tasa wani gwamna a gaba, tana mamayansa

Talala: Hukumar EFCC ta tasa wani gwamna a gaba, tana mamayansa

Ranar kin dillanci: Jami’an EFCC sun shirya ma gwamnan jahar Ekiti tarkon rago
NAIJ.com
Mailfire view pixel