Yanzu Yanzu: Sanata Dino Melaye ya bukaci ban-hakuri daga shugaba Buhari kan zagin da akayiwa majalisa

Yanzu Yanzu: Sanata Dino Melaye ya bukaci ban-hakuri daga shugaba Buhari kan zagin da akayiwa majalisa

Sanata Dino Melaye ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya ba majalisar dokoki hakuri kan abunda ya bayyana a matsayin cin mutunci ga majalisar masu rinjaye.

Ya bayyana cewa shugaban kasar yayi ikirarin cewa bai san abunda yan majalisan da dama ke yi ba.

Sanata Dino Melaye ya yi nuni ga cewa shugaban kasa ya ci mutuncin majalisa ta gidan talbijin din Channels da AIT inda yace bai san abunda suke yi ba sannan kuma cewa da yawansu sun shafe sama da shekaru 10 amma duk da haka babu abun nunawa.

Wannan kalami cin mutunci ne ga majalisa kamar yadda sanatan ya bayyana.

“Ina kira ga shugaban kasa da ya bayar da hakuri akan jawabi da yayi game da majalisar dokoki."

A baya NAIJ.com ta rahoto cewa Sanata Dino Melaye ya sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa PDP, hakan ya kasance ne bayan ya dawo majalisa a ranar Laraba, 30 ga watan Mayu.

KU KARANTA KUMA: Yan PDP da yawa sun sauya sheka zuwa APC a Jigawa

Sai dai jam'iyyar ta APC ta musanta hakan domin a cewarta bai sanar da su ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
2019: Kungiya ta sha alwashin kawo wa Atiku kuri’u miliyan 10

2019: Kungiya ta sha alwashin kawo wa Atiku kuri’u miliyan 10

2019: Kungiya ta sha alwashin kawo wa Atiku kuri’u miliyan 10
NAIJ.com
Mailfire view pixel