Salah ya tafi Spain neman magani

Salah ya tafi Spain neman magani

Shahararren dan wasan kwallon kafar nan wanda tauraruwar shi take haskawa a yanzu, Mohammed Salah, ya isa kasar Spain domin cigaba da karbar magani dalilin raunin da yaji a lokacin da suka kara wasan karshe na cin kofin zakarun turai tsakanin kungiyarsa ta Liverpool da kuma kungiyar Real Madrid

Salah ya tafi Spain neman magani
Salah ya tafi Spain neman magani

Shahararren dan wasan kwallon kafar nan wanda tauraruwar shi take haskawa a yanzu, Mohammed Salah, ya isa kasar Spain domin cigaba da karbar magani dalilin raunin da yaji a lokacin da suka kara wasan karshe na cin kofin zakarun turai tsakanin kungiyarsa ta Liverpool da kuma kungiyar Real Madrid.

DUBA WANNAN: Za a caji Ramos Pounds biliyan 1, saboda dukan Mohammed Salah da yayi

Salah wanda ya tafi birnin Valencia na kasar Spain, yaki ya saurari manema labarai a lokacin da suke ta kokarin ganin sunyi masa tambayoyi.

'Yan jaridar na kasar Spain sun nemi su san ko dan wasan zai iya buga wasan gasar cin kofin duniya, sannan kuma sun so su tambaye shi ko yana ganin da gangan ne Sergio Ramos ya ji masa ciwo.

Sergio Ramos wanda shine yayi sanadiyyar jiwa Salah ciwo, yayi gaggawar wallafa wani sako a shafinsa na yanar gizo wato Twitter, inda yake yiwa Salah fatan samun lafiya cikin gaggawa.

An tabbatar da cewar fiye da mutane 500,000 suka goyi bayan a hukunta Ramos a shafin su na koke na yanar gizo petition.org, da zargin cewar Ramos yaji wa Salah ciwo da gangan ne.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel