Osinbajo ya yabawa Dangote dangane da Gudunmuwar Motoci 150 da ya bai wa Hukumar 'Yan sandan Najeriya

Osinbajo ya yabawa Dangote dangane da Gudunmuwar Motoci 150 da ya bai wa Hukumar 'Yan sandan Najeriya

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya yabawa shugaban gidauniyar Dangote, Alhaji Aliko Dangote, dangane da gudunmuwar motocin aiki 150 da ya bai wa hukumar 'yan sandan Najeriya.

Mataimakin shugaban kasar yake cewa, gudunmuwar motocin za ta tallafa kwarai da aniyya wajen tunkarar matsalolin tsaro a kasar nan.

A yayin da mataimakin shugaban kasar ke nuna godiyar gwamnatin tarayya ya bayyana cewa, Dangote ya ciri tuta gami da kasancewa zakaran gwajin dafi cikin 'yan kasuwar kasar nan sakamakon rawar da yake ci gaba da takawa domin habakar tattalin arziki a Najeriya.

Yake cewa, gwamnatin Najeriya na da bukatar mutane makamancin Dangote da za ta hada gwiwa da shi wajen bukasa tattalin arziki da kuma samar da aikin yi ga matasa.

Osinbajo ya bayyana cewa wannan gudunmuwar motoci da attajirin ya bai wa hukumar 'yan sandan kasar ta yi fice wadda ba a taba samun makamanciyar ta ba, inda yake kiran sauran 'yan Najeriya akan hada gwiwa da gwamnatin tarayya domin samar da ingataccen ci gaba da kuma bunkasa tattalin arziki.

Osinbajo ya yabawa Dangote dangane da Gudunmuwar Motoci 150 da ya bai wa Hukumar 'Yan sandan Najeriya
Osinbajo ya yabawa Dangote dangane da Gudunmuwar Motoci 150 da ya bai wa Hukumar 'Yan sandan Najeriya

Osinbajo ya yabawa Dangote dangane da Gudunmuwar Motoci 150 da ya bai wa Hukumar 'Yan sandan Najeriya
Osinbajo ya yabawa Dangote dangane da Gudunmuwar Motoci 150 da ya bai wa Hukumar 'Yan sandan Najeriya

Osinbajo ya yabawa Dangote dangane da Gudunmuwar Motoci 150 da ya bai wa Hukumar 'Yan sandan Najeriya
Osinbajo ya yabawa Dangote dangane da Gudunmuwar Motoci 150 da ya bai wa Hukumar 'Yan sandan Najeriya

Osinbajo ya yabawa Dangote dangane da Gudunmuwar Motoci 150 da ya bai wa Hukumar 'Yan sandan Najeriya
Osinbajo ya yabawa Dangote dangane da Gudunmuwar Motoci 150 da ya bai wa Hukumar 'Yan sandan Najeriya

A nasa jawabin yayin mika wannan gudunmuwa, gawurtaccen attajirin ya bayyana cewa wannan goma ta arziki ta zo ne a sakamakon yadda tsaro da zaman lafiya ke tafiya hannu da hannu wajen bunkasa tattalin arziki.

Legit.ng ta fahimci cewa, gidauniyar Dangote ta matsa kaimi wajen bunkasa rassa hudu na kasar nan da suka hadar da; lafiya, ilimi, tattalin arziki da kuma bayar da agajin ibtila'in annoba, inda take salwantar da sama da Naira Biliyan 10 a duk shekara wajen aiwatar da hakan.

Dangote ya sha alwashin cewa akwai yiwuwar gidauniyar sa ta sake bayar da wata gudunmuwar makamanciyar wannan a yayin da hukumar tayi tattali gami da alkinta wanda ta samu a halin yanzu.

KARANTA KUMA: Hukumar Sojin Ruwa ta cafke Lita 386, 000 ta 'Danyen Man Fetur da Mutane 9 a garin Delta

A nasa bangaren Sufeto Janar na 'Yan sanda, Ibrahim Idris, ya yi alkawalin alkinta motocin gami da bayar da tabbacin sa akan amfani da su bisa ga manufar wannan gudunmuwar.

Ya kuma bayar da tabbacin sa na cewar hukumar 'yan sanda ba za ta bai wa 'yan Najeriya kunya ba wajen inganta tsaro da zaman lafiya a fadin kasar nan.

Ya kara da cewa, babbar manufa ta wannan gudunmuwa ita ce kara bunkasa hukumar 'yan sanda ta kasar nan gami da inganta mu'amalan ta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel