Hukumar EFCC ta tsare Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Ramalan Yero

Hukumar EFCC ta tsare Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Ramalan Yero

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito mun samu rahoton cewa, hukumar hana yiwa tattalin arziki zagon kasa ta tsare tsohon gwamnan jihar Kaduna, Alhaji Ramalan Yero a ofishin ta na jihar Kaduna.

Jaridar ta ruwaito cewa, hukumar ta tsare tsohon gwamnan ne tare da Abubakar Gaya Haruna tsohon shugaban jam'iyyar PDP na jihar, tsohon sakataren gwamnatin jihar Hamza Ishaq da kuma tsohon Minista, Nuhu Somo Wya.

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan mutane hudu sun saba gabatar da kansu a gaban hukumar tun watanni biyu da suka gabata domin gudanar da bincike a kansu.

Hukumar EFCC ta tsare Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Ramalan Yero
Hukumar EFCC ta tsare Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Ramalan Yero

Wata majiyar rahoto daga hukumar ta bayyana cewa, an garkame tsaffin shugabannin ne a yayin da suka gabatar da kansu a safiyar yau ta Laraba sakamakon gurfana da za su yi gaban Kuliya a gobe Alhamis.

KARANTA KUMA: Katin Zabe Da Na'urar sa ne suka taka rawar gani wajen nasara ta a Zaben 2015 - Buhari

Legit.ng ta fahimci cewa, ana zargin tsaffin shugabannin ne cikin almundahanar Naira Miliyan 750 na kudaden yakin neman zabe na jam'iyyar PDP a shekarar 2015 da ta gabata.

A makon da ya gabata ne aka titsiye tsohon gwamnan da sauran shugabannin uku yayin da suka rattaba hannu kan wasu takardu cikin wani ɓangare na gudanar da bincike a kansu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel